Connect with us

Kasuwanci

Gwamnatin Jigawa Za Ta Kashe Naira Biliyan 3.5 Wajen Gina Shaguna A Farm Centre

Published

on

Gwamnatin Jihar Jigawa ta fara aikin gina shaguna guda dubu daya a cibiyar kasuwanci ta Farm Centre da ke Kano, wanda zai lakume  kudi Naira Biliyan Uku da rabi (N3.5bn), domin bunkasa kudaden shiga na cikin gida na jihar.

 

Shugaban Kungiyar Hadaka kan Tsaro, Zaman Lafiya da Warware Rikice-rikice a Jihar Jigawa, Muhammad Musbahu Basirka, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a sakatariyar NUJ da ke Dutse, babban birnin jihar.

 

Ya bayyana cewa, hukumar EFCC ce ta mika filin hannun gwamnatin jihar Jigawa a matsayin wani bangare na dawo da kadarorin da jihar ta gada  daga tsohuwar jihar Kano.

 

Ya ce: “Wannan fili da ke a tsakiyar  birnin Kano, na daga cikin kadarorin da jihar Jigawa ta gada bisa tsarin raba kadarori da filaye da aka yi bayan kirkar jihar Jigawa daga tsohuwar jihar Kano a watan Agustan 1991.”

 

Bayan tattaunawa da masana, shugabannin al’umma da kuma masu ruwa da tsaki, muna sanar da jama’ar jihar Jigawa cewa gwamnatinmu ta yanke shawarar amfani da wannan fili mai muhimmanci domin amfanar kowa da kowa.

 

Manufar ita ce kara habaka kudaden shiga na cikin gida na jihar, kasancewar filin na dag cikin muhimman wuraren kasuwanci na Kano. Gwamnatinmu na fuskantar bukatar fadada hanyoyin samun kudaden shiga ba tare da dogaro kacokan ga kasafin kudi na kasa”.

 

Yayin da ya ke kira ga ‘yan asalin jihar da sauran mazauna da su rungumi wannan cigaba da fahimta da hadin kai, Musbahu Basirka ya ja hankalin jama’a da  a  guji siyasantar da wannan lamarin.

 

Duk da haka muna maraba da shawarwari masu amfani kan hanyoyin da za a fi amfana da wannan aiki mai matukar muhimmanci domin dorewar ci gaba ga al’umma.” In ji shi. 

 

Mu a matsayinmu na wakilan kungiyoyin fararen hula, za mu kasance cikin tsaka-tsaki wajen sa ido da tabbatar da cewa an yi  aiki mai inganci, tare da yin nazari lokaci-lokaci domin tabbatar da gaskiya da adalci ” in ji Basirka.

 

Usman Muhammad Zaria

 

 

Labarai

Labarai4 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai1 day ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai1 day ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai1 day ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara