Labarai
Daruruwan Jama’a Sun Halarci Sallar Jana’izar Marigayi Sarkin Gusau
Daruruwan mutane daga sassa daban-daban na Jihar Zamfara da wajen ta sun halarci Sallar jana’izar marigayi Sarkin Gusau, Dr. Ibrahim Bello, wanda ya rasu a daren Alhamis bayan gajeruwar rashin lafiya.
An gudanar da Sallar jana’izar ne a Masallacin Jumu’a na Gusau da ke Kanwuri, inda Mataimakin Babban Limamin masallacin, Malam Abdulkareem Umar, ya jagoranci addu’o’in.

Daga cikin manyan baki da suka halarta har da Gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal, wanda ya bayyana marigayin a matsayin Uba ga kowa, shugaba mai son zaman lafiya, kuma mutum mai hikima wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaba da hadin kan jihar.
Gwamna Lawal ya nuna alhini matuka game da rasuwar Sarkin, inda ya yi addu’ar Allah ya jikansa ya gafarta masa. Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su yi koyi da kyawawan halayen marigayin na tawali’u, adalci da kokarin tabbatar da zaman lafiya.

Haka zalika, mataimakin gwamna, Mani Malam Mummuni, sakataren gwamnatin jihar, manyan jami’an gwamnati, ‘yan majalisar dokoki ta jiha, sarakuna, malamai da daruruwan al’ummar gari daga fannoni daban-daban sun halarci Sallar.
Su ma ‘yan majalisar wakilai da ke wakiltar Maru/Bungudu da kuma Gusau a Majalisar Wakilai ta Tarayya, Dr. Abdulmalik Zannan Bungudu da Kabiru Ahmad Maipalace, sun halarci jana’izar.
Haka kuma dukka sarakunan masu daraja ta farko a Jihar Zamfara da hakimai daban-daban sun halarci sallar jana’izar.
Marigayi Sarkin Gusau, Dr. Ibrahim Bello, wanda ya hau karagar mulki a shekarar 2004, ya shahara fannin ilimi, da kuma kokarin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Zamfara.
Rasuwarsa ta zamto babban rashi ga masarautar da ma al’ummar jihar baki ɗaya.
An binne shi a makabartar Kwata da ke Gusau, yayin da ake ci gaba da zuwa ta’aziyya da yi masa addu’a.
Daga Aminu Dalhatu
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
