Connect with us

Kasuwanci

Gwamnatin Jigawa Za Ta Hada Hannu Da Masana Harkar Dabino Na Kasar Saudiyya

Published

on

A ci gaba da kokarinta na samun tagomashi a fannin tattalin arziki da ci gaban jihar ta hanyar kawo sauyi a harkar noma, gwamnatin jihar Jigawa na shirin hada gwiwa da wani kamfani da ke samar da dabino  da bayar da shawarwari a harkar noma, wanda ke da ofishi a Najeriya a kasar Saudiyya domin bunkasa noman dabino a jihar.

Gwamna Malam Umar Namadi ne ya bayyana hakan a yayin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga daya daga cikin manyan kamfanonin noma na kasar Saudiyya, wadanda suka kware a harkar noman dabino da sarrafa gonaki, karkashin jagorancin Abdul’aziz Abdurrahman Al-Awf, wadanda suka kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati dake Dutse.

Babban makasudin ziyarar ita ce tattaunawa kan dabarun hadin gwiwa da nufin bunkasa noman dabino a Jigawa, ta hanyar bunkasar fasahar noma, da musayar ra’ayoyi, da zuba jari a fannin noma.

Da yake jawabi a wajen taron, Abdul’aziz Al-Awf ya bayyana kudirin kamfaninsa na kawo sabbin dabarun noman zamani a jihar Jigawa, tare da tabbatar da samar da dabino a duk shekara maimakon noman rani, inda ya nuna cewa hadin gwiwar zai kunshi horar da manoma sosai, da karfafawa matasa gwiwa, da kuma bullo da wasu nau’o’in dabino masu kima da yawan amfanin gona a kasar Saudiyya.

Wannan hadin gwiwa ba wai kawai zai kara yawan dabino da ake nomawa a Jigawa ba ne, har ma da inganta shi, wanda hakan zai sa jihar ta zama cibiyar noman dabino a Najeriya da Afrika,” inji shi.

Gwamna Namadi ya bayyana cikakken goyon bayan gwamnatinsa ga shirin, yana mai cewa ya yi daidai da tsarin bunkasa noma na jihar.

Muna maraba da ku zuwa jihar Jigawa kuma mun yaba da sha’awar ku ta yin aiki da mu. A matsayinmu na gwamnati mun jajirce sosai wajen wannan hadin gwiwa domin zai amfani al’ummarmu matuka. Ziyarar ku da kuma shirye-shiryen ku na hadin gwiwa da mu kan samar da noman dabino a fadin jihar nan, tare da inganta noman alkama, sun yi dai dai da burinmu na bunkasa noma.”

Ya bayyana  Jigawa a matsayin kan gaba wajen noman alkama a Najeriya, tare da jaddada manufarsa ta fadada noman dabino a jihar.

Gwamna Namadi ya jaddada shirin gwamnatinsa na samar da duk wani abu da ake bukata domin ganin an samu nasarar aiwatar da aikin.

Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa hadin gwiwar zai samar da fa’ida sosai, tare da sanya Jigawa a matsayin kan gaba a masana’antar dabino ta duniya.

Mun himmatu wajen mai da jihar Jigawa cibiyar noman dabino, ba kawai don amfanin gida ba har ma da fitar da shi zuwa kasashen waje domin bunkasa tattalin arzikin jihar. 

A yayin ziyarar, tawagar  ta Saudiyya tare da wakilan kamfanin Netay Agro-Tech sun zagaya wurare daban-daban a fadin jihar domin tantance dabino da ake da su.

Abubakar Musa Bamai, Shugaban Kamfanin Netay Agro-Tech, ya bayyana dimbin ayyukan da aka riga aka yi, wadanda suka hada da nazarin kasa da tuntubar juna da cibiyoyin bincike.

Ya sanar da cewa nau’in dabino guda hudu da ake nema, wato Mejdool (Meju), Barhi (Bari), Sukkari (Sukari), da Ajwa—an bayyana su a matsayin wadanda suka dace don noma mai inganci a Jigawa.

 

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai8 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara