Ilimi
Gwamnatin Jihar Kano Ta Fara Rangadin Tantance Yaran Da Ba Sa Zuwa Makaranta
Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta fara rangadin tantancewa a kauyukan jihar, gabanin shirin wayar da kan al’umma game da yaran da ba su zuwa makaranta.
Ziyarar na da nufin gano musabbabin wannan matsala tare da nemo mafita ta hanyar hada kai tsakanin al’umma.

Kididdigar da Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar na nuna da cewa, Kano tana da kimanin yara 837,479 da ba sa zuwa makaranta, adadi mai ban mamaki da jihar ke kokarin magancewa.
Tawagar tantancewar, karkashin jagorancin jami’a mai kula da ilimin yara mata ta jihar, Hajiya Amina Kassim, ta ziyarci kauyuka da dama, inda ta tattauna da iyaye, da shugabannin gargajiya, da malaman addini.

“Tawagar ta gano muhimman abubuwan da ke haddasa yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a yankunan karkara, ciki har da talauci, da rashin tsaro, da kuma al’adun zamantakewa”
Mataimakin shugaban kwamitin gudanarwa na makarantun jihar SBMC, Alhaji Garba Adamu Wudil, ya ce ta hanyar hada kai da al’ummomin yankin da masu ruwa da tsaki, gwamnati na da burin kara fahimtar matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma kokarin samar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa.

Hakimin kauyen Kafin Malamai a karamar hukumar Garko Mukhtar Aliyu da wakilin hakimin kauyen Bange na Wudil Ya’u Ibrahim Bange sun yabawa kokarin gwamnati mai ci na gyara fannin ilimi.
Sun yi kira ga gwamnati da ta kara samar da karin makarantun sakandire a cikin al’umma domin daukar adadin daliban da suka kammala karamar sakandare (JSS) duk shekara.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, rangadin tantancewar wani muhimmin mataki ne na samar da ingantattun dabaru don rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar Kano.
Daga Khadija Aliyu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
