Connect with us

Kasuwanci

Gwamnatin Jigawa Za Ta Hada Hannu Da Masana Harkar Dabino Na Kasar Saudiyya

Published

on

A ci gaba da kokarinta na samun tagomashi a fannin tattalin arziki da ci gaban jihar ta hanyar kawo sauyi a harkar noma, gwamnatin jihar Jigawa na shirin hada gwiwa da wani kamfani da ke samar da dabino  da bayar da shawarwari a harkar noma, wanda ke da ofishi a Najeriya a kasar Saudiyya domin bunkasa noman dabino a jihar.

Gwamna Malam Umar Namadi ne ya bayyana hakan a yayin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga daya daga cikin manyan kamfanonin noma na kasar Saudiyya, wadanda suka kware a harkar noman dabino da sarrafa gonaki, karkashin jagorancin Abdul’aziz Abdurrahman Al-Awf, wadanda suka kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati dake Dutse.

Babban makasudin ziyarar ita ce tattaunawa kan dabarun hadin gwiwa da nufin bunkasa noman dabino a Jigawa, ta hanyar bunkasar fasahar noma, da musayar ra’ayoyi, da zuba jari a fannin noma.

Da yake jawabi a wajen taron, Abdul’aziz Al-Awf ya bayyana kudirin kamfaninsa na kawo sabbin dabarun noman zamani a jihar Jigawa, tare da tabbatar da samar da dabino a duk shekara maimakon noman rani, inda ya nuna cewa hadin gwiwar zai kunshi horar da manoma sosai, da karfafawa matasa gwiwa, da kuma bullo da wasu nau’o’in dabino masu kima da yawan amfanin gona a kasar Saudiyya.

“Wannan hadin gwiwa ba wai kawai zai kara yawan dabino da ake nomawa a Jigawa ba ne, har ma da inganta shi, wanda hakan zai sa jihar ta zama cibiyar noman dabino a Najeriya da Afrika,” inji shi.

Gwamna Namadi ya bayyana cikakken goyon bayan gwamnatinsa ga shirin, yana mai cewa ya yi daidai da tsarin bunkasa noma na jihar.

“Muna maraba da ku zuwa jihar Jigawa kuma mun yaba da sha’awar ku ta yin aiki da mu. A matsayinmu na gwamnati mun jajirce sosai wajen wannan hadin gwiwa domin zai amfani al’ummarmu matuka. Ziyarar ku da kuma shirye-shiryen ku na hadin gwiwa da mu kan samar da noman dabino a fadin jihar nan, tare da inganta noman alkama, sun yi dai dai da burinmu na bunkasa noma.”

Ya bayyana  Jigawa a matsayin kan gaba wajen noman alkama a Najeriya, tare da jaddada manufarsa ta fadada noman dabino a jihar.

Gwamna Namadi ya jaddada shirin gwamnatinsa na samar da duk wani abu da ake bukata domin ganin an samu nasarar aiwatar da aikin.

Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa hadin gwiwar zai samar da fa’ida sosai, tare da sanya Jigawa a matsayin kan gaba a masana’antar dabino ta duniya.

“Mun himmatu wajen mai da jihar Jigawa cibiyar noman dabino, ba kawai don amfanin gida ba har ma da fitar da shi zuwa kasashen waje domin bunkasa tattalin arzikin jihar. 

A yayin ziyarar, tawagar  ta Saudiyya tare da wakilan kamfanin Netay Agro-Tech sun zagaya wurare daban-daban a fadin jihar domin tantance dabino da ake da su.

Abubakar Musa Bamai, Shugaban Kamfanin Netay Agro-Tech, ya bayyana dimbin ayyukan da aka riga aka yi, wadanda suka hada da nazarin kasa da tuntubar juna da cibiyoyin bincike.

Ya sanar da cewa nau’in dabino guda hudu da ake nema, wato Mejdool (Meju), Barhi (Bari), Sukkari (Sukari), da Ajwa—an bayyana su a matsayin wadanda suka dace don noma mai inganci a Jigawa.

 

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara