Connect with us

Kasuwanci

Al’ummar Jigawa Sun Bukaci Gwamnati Ta Yi Koyi Da Shirin NG-CARES Wajen Tallafawa Mabukata

Published

on

Al’ummar Jihar Jigawa sun yi kira ga Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi da ya yi amfani da kyawawan tsarin da gaskiya wajen zabar wadanda za su ci gajiyar shirye-shiryen bada tallafin karfafa sana’o’i.

Sun kuma bukaci gwamnatin jihar da ta yi amfani da tsarin bayar da tallafin karfafa al’umma ma gwamnatin tarayya na (FADAMA) a  dukkan shirye shiryenta ta bada tallafi,  domin ganin al’ummar jihar sun ci gajiyar ayyukan gwamnati.

Wani shugaban al’ummar yankin Walewale a karamar hukumar Garki, Malam Haruna Abdullahi, ya ce, hanyar da shirin FADAMA na gwamnatin tarayya ya yi amfani da ita ya tabbatar da cewa tallafin ya isa ga masu bukata.

A cewarsa, tsarin ya kawar da son zuciya da siyasa, wanda hakan ya  yi tasiri matuka ga al’umma.

“Mun ga yadda shirin FADAMA kkarkashin shirin gwamnatin tarayya na G-CARES ya samu damar tallafawa manoma na hakika da sauran mutanen da suka cancanta, idan aka yi amfani da wannan tsari a duk wasu tsare-tsare na karfafawa, zai kawo ci gaba na hakika a jihar Jigawa.”

Wani mazaunin garin, Usman Alhaji na Arbun a karamar hukumar Auyo, ya kara da cewa daukar tsarin zaben wadanda suka cancanta zai kara wa gwamnatin jihar kima a idon  jama’a.

Sun bukaci Gwamna Namadi da ya yi amfani da wannan tsari ga sauran shirye-shiryen karfafawa a jihar, tare da tabbatar da cewa tallafin gwamnati na isa ga wadanda suka fi bukata.

Shi ma da yake jawabi, shugaban kwamitin riko na shirin FADAMA CARES, Dakta Saifullahi Umar ya bayyana cewa, shirin na NG-CARES  an tsara shi ne domin dakile matsin tattalin arzikin da annobar Corona

. ta haifar.

Dakta Saifullahi ya ce, abu na 2 wanda aka aiwatar ta hanyar shirin FADAMA, yana mai da hankali  ne kan tallafin noma da inganta rayuwa, ta hanyar yin amfani da kyakkyawan tsari wajen zabo wadanda suka dace su ci gajiyar shirin.

 

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara