Labarai
Gwamnatin Jigawa Ta Raba Tallafin Kayayyakin Sana’o’i A Karamar Hukumar Gagarawa
Gwamnatin Jihar Jigawa za ta kafa ƙananan masana’antu a karamar hukumar Gagarawa.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan yayin kaddamar da rabon kayayyakin bunkasa tattalin arziki ga wasu daga cikin al’ummar Gagarawa.
Malam Umar Namadi ya yi bayanin cewar, masana’antun za su hada da na sarrafa shinkafa da sauransu.

Yana mai cewar hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasa marasa aikin yi a yankin.
Kazalika, Gwamnan yace gwamnatin jihar za ta ware kudi a kasafin kudin shekarar badi don gina hanyar mota daga Medu zuwa Dandidi zuwa Madaka, domin saukaka sufuri ga al’ummar yankin.

Baya ga kaddamar da tallafin, Malam Umar Namadi, ya bude wasu ayyukan ci gaba ciki har da makarantar Tahfizul Qur’ani ta Hajiya Maryam Namadi da babban dakin taro da kuma gyaran babban masallacin Gagarawa.
A halin yanzu, mutane sama da 2,000 ne aka zakulo domin cin gajiyar kayayyakin tallafin.

Kayayyakin sun hada da tallafin naira miliyan 70 da babura da injinan dinki da na niƙa.
Sai kuma kekuna ga ɗalibai da injinan yin taliya da kuma shigar da makiyaya sama da 1,000 cikin makarantun ‘yayan fulani makiyaya.

Taron ya samu halartar shugaban majalisar dokokin jihar da wasu daga cikin ‘yan majalisar zartarwar jihar, da dai sauransu.
Usman Mohammed Zaria
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
