Fasaha
Gwamnan Kano Ya Kaddamar da Shirin Dashen Bishiyoyi
Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na yaki da gurbacewar kasa, zaizayar kasa da sauran kalubalen muhalli.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin bikin kaddamar da wani katafaren shirin dashen itatuwa, inda za a dasa itatuwa miliyan 5 da rabi a fadin jihar, wanda aka gudanar a karamar hukumar Makoda.
Ya ce babban makasudin wannan shirin shi ne a magance dimbin kalubalen muhalli da ke addabar al’ummar jihar Kano.
Gwamna Yusuf ya jadadda cewa wadannan kalubalen na haifar da babbar matsala ga al’umma.
Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta bayar da duk wani tallafin da ya dace don shayar da ‘ya’yan itatuwan, ta yadda za su yi girma da kuma cim ma burin da aka yi niyya. Wannan tallafi yana da mahimmanci don nasarar shirin.
Ya bukaci dukkan shugabannin kananan hukumomi 44, shugabannin gargajiya, da jami’an ci gaban al’umma (CDOs) da su sanya hannu a cikin wannan shirin, inda ya ce shigar su na da matukar muhimmanci wajen cimma manufofin shirin.
“Idan aka kula da kyau itatuwan da aka dasa ta wannan shiri za su taka rawar gani wajen magance sauyin yanayi da batutuwan da ke da alaka da hakan. Hakan ya yi dai-dai da manyan manufofin jihar Kano.”
Kwamishinan Muhalli, Dr. Dahiru Mohammad Hashim, ya yaba da kudurin Gwamna Yusuf na tallafawa kokarin ma’aikatar wajen dakile matsalolin muhalli.
Sarkin Dawakin Mai Tuta Alhaji Mohammad Bello Abubakar, wanda ya wakilci Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi II ya jaddada goyon bayan Masarautar kan shirin dashen itatuwa.
Taron ya gabatar da bayar da kyautuka ga mutanen da suka bayar da gudunmawa sosai wajen tallafawa al’ummarsu.
Wannan amincewa yana aiki azaman abin ƙarfafawa ga wasu don shiga cikin ayyukan muhalli.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
