Connect with us

Labarai

Gwamna Yusuf Ya Rantsar Da Sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe Ta Jihar Kano

Published

on

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da Barista Sa’idu Yahaya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC).

An gudanar da wannan gajeren bikin ne a gidan gwamnati na Kano, inda Babban Lauya kuma Kwamishinan Shari’a na jihar, Barista Haruna Isa Dederi, ya jagoranci rantsar da shi.

Idan za a tuna Gwamna Yusuf ya gabatar da sunan Sa’idu Yahaya ga Majalisar Dokokin Jihar Kano domin tantancewa da tabbatarwa bisa tsarin doka, inda daga bisani majalisar ta amince da nadin nasa.

Barista Sa’idu Yahaya ƙwararren masani ne a fannin yaƙi da cin hanci, wanda ya goge a aikinsa shekaru sama da 18. Ya yi aiki a Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Sauran Laifuka Masu Alaƙa  (ICPC), inda ya kware a bincike,  da gano kadarori.

Da yake taya shi murna, Gwamna Yusuf ya nuna kwarin gwiwa cewa Yahaya zai sake fasalta PCACC tare da ƙarfafa jajircewar gwamnatin jihar wajen yaƙar cin hanci da wanzar da gaskiya a cikin mulki.

Ya yi kira a gare shi da ya gudanar da aikinsa bisa gaskiya da adalci,  inda ya ƙara jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tsayawa kan gaskiya da riƙon amana a hidimar jama’a.

A jawabinsa bayan an rantsar da shi, Barista Yahaya ya yi alƙawarin tabbatar da amincewar da aka nuna gare shi, inda ya ce zai ƙara kaimi wajen rage cin hanci, dawo da kadarorin da aka wawure, da tabbatar da adalci ga dukkan jama’ar Kano.

Hukumar PCACC, wacce aka kafa domin karɓar ƙorafe-ƙorafen jama’a da kuma yaƙar cin hanci a matakin jiha, ana sa ran za ta taka muhimmiyar rawa a ƙarƙashin shugabancin Sa’idu Yahaya wajen cike gibin da hukumomin tarayya suka bari.

 

Abdullahi Jalaluddeen 

Labarai

Labarai14 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai2 days ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai2 days ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara