Labarai
Gwamna Yusuf Ya Kafa Kwamitin Bincike Kan Mutumin Da Ake Tuhuma Da Safarar Miyagun Kwayoyi
A kokarinsa na gano hakikanin dalilan da suka sa aka bayar da beli ga wani sanannen mai safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Dan Wawu, da aka ce an sako shi bisa umarnin Kwamishinan Sufuri na Kano, Ibrahim Ali Namadi, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da wani kwamiti na mutum takwas domin gudanar da bincike mai zurfi.
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim ne ya kaddamar da kwamitin a madadin gwamnan.
An umurci kwamitin da ya gudanar da binciken cikin mako guda, domin gano hakikanin abin da ya faru da kuma ba da shawarwari kan matakin da ya dace a dauka.
Shugaban kwamitin shi ne Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Shari’a da Dokoki, Barista Aminu Hussaini, yayin da Mambobin kwamitin suka hada da Barista Hamza Haladu, Barista Hamza Nuhu Dantani, Darakta Janar na Hukumar Ayyuka na Musamman, Manjo Janar Muhammad Sani (rtd), Comrade Kabiru Dakata, da Farfesa Mamun Mustapha daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil.
Sauran mambobin sun hada da Alhaji Abdullahi Mahmud Umar, Kwamishina II na Hukumar Kula da Ma’aikata, da Hajiya Bilkisu Shehu Mai Mota, Babbar Sakatariya a Sashen Gudanarwa da Sauran Ayyuka na ofishin Sakataren Gwamnatin .Jihar, wadda za ta rike matsayin Sakatariya ga kwamitin.
Gwamna Yusuf ya bayyana damuwarsa matuka kan zargin da ake yi, inda ya sake jaddada kudirinsa na yaki da safarar miyagun kwayoyi da duk wani nau’in barna a cikin al’umma.
Sakataren Gwamnatin Jihar ya bayyana kwarin gwiwarsa kan mambobin kwamitin, yana mai cewa an zabo su ne bisa cancanta, kwarewa, karsashi, da kuma kwarin gwiwar cewa za su gudanar da wannan aiki yadda ya kamata.
Abdullahi Jalaluddeen
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
