Labarai
Matawalle Ya Bada Tallafin Kudi Da Kayayyakin Abinci Ga Iyalan Marigayi Sarkin Gusau
Ministan Harkokin Tsaron Ƙasa, Dakta Bello Mohammed Matawalle, ya baiwa iyalan marigayi Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, gudummawar naira miliyan biyar da kuma kayan abinci, bayan rasuwarsa a ranar Alhamis da ta gabata a birnin Abuja sakamakon gajeruwar rashin lafiya.
Dakta Matawalle, ya bayyana alhininsa bisa wannan rashi na Mai Martaba.

Baya ga gudummawar kuɗi, ministan ya kuma bada buhunan shinkafa 20, gero 10, masara 10 da kuma dawa 10 ga iyalan mamacin.
Wata tawaga mai ƙarƙashin jagorancin Sanata Hassan Muhammad Nasiha, tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara a zamanin mulkin Matawalle ne suka miƙa gudummawar a madadin ministan.

Dakta Matawalle ya bayyana marigayi Sarkin Gusau a matsayin shugaba mai ɗabi’a ta gari, wanda ya kasance mai sauƙin kai da tausayi a duk tsawon mulkinsa.
Ya ambato irin jajircewarsa wajen kula da marayu da taimaka musu wajen samun ilimi, inda da dama daga cikinsu suka zama mutane masu amfani a cikin al’umma.

“Rasuwar Sarkin ta bar gibidmai wuyar cika,” in ji Matawalle, yana mai addu’ar Allah Ya jikansa da rahama, tare da baiwa iyalan haƙurin jure rashin.
Da yake karɓar tawagar da gudummawar a madadin iyalan, Hakimin Sunami, Alhaji Mainasara Bello Ciroman Gusau, ya nuna godiya ga ministan bisa wannan gudummawar.

Ya ce masarautar za ta ci gaba da tunawa tare da girmama goyon bayan da Matawalle ke baiwa masarautu, musamman a lokacin da yake gwamna.
Tawagar ta haɗa da fitattun mutane irinsu Ibrahim Umar Dangaladima, Sakataren APC na Jiha; Bashir Idris Ataka, Sakataren Walwala na APC; Mallam Yusuf Idris Gusau, Sakataren Yaɗa Labarai na APC; Ibrahim Maigandi Danmalikin Gidan Goga, Mai ba Minista shawara kan harkokin siyasa, da sauransu.
Haka kuma, Sheikh Tukur Sani Jangebe ya yi addu’ar Allah ya ji ƙan marigayi Sarkin Gusau.
Daga Aminu Dalhatu
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
