Labarai
Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Kaddamar Da Dashen Itatuwa Na Bana
Gwamnatin Jihar Jigawa ta kaddamar da dashen itatuwa na shekarar 2025 tare da sabunta kudirin farfado da fiye da hekta 5,000 da ta lalace a fadin jihar.
Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a wajen bikin kaddamar da shirin da aka gudanar a shatale-tale na Pentagon da ke Dutse babban birnin jihar.
Ya bayyana aikin dashen itatuwan a matsayin ɗaya daga cikin alkawuran da gwamnatinsa ta ɗauka domin ci gaban al’umma, inda ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen raya muhalli da kare shi.

Ya ce: “Wannan yana da alaƙa da manufofinmu da suka shafi ƙaddamar da tsare-tsare da suka dace da kare muhalli, da ƙarfafa juriya da dorewar muhalli, da kuma inganta rayuwa mai tsafta da dorewa ga al’umma.”
Yayin da yake bayyana muhimmancin shirin, Malam Umar Namadi ya jaddada cewa kalubalen muhalli kamar ambaliya, sahara, sare itatuwa da kuma rashin daidaiton kula da shara na cigaba da barazana ga rayuwar mutane a jihar.

“Wannan barazana na shafar rayuwarmu ta yau da kullum, abincinmu, lafiyarmu, da kuma zaman lafiyar al’ummomi da dama a fadin jihar. Ya zama wajibi mu hada kai domin yaki da duk wani nau’in lalacewar muhalli.” In ji Gwamnan.
Gwamnan wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim ya wakilta, ya bayyana cewa ana amfani da shirin ACReSAL wajen farfado da ƙasa ta hanyar dasa itatuwa, da kiyayewa da kuma tsarin noma da gandun daji.

“Yanzu haka, gwamnatin jihar Jigawa ta hanyar shirin ACReSAL na kokarin farfado da hekta 5,000 a wurare 27 a fadin jihar, ta hanyar samar da katanga ta itatuwa, wuraren kiwo da tsarin gandun daji. Mun riga mun fara sauya yanayin da ake ciki ta hanyar wadannan matakan da za a iya auna su.”
Ya kuma bayyana cewa an duba dokoki guda biyar da suka shafi muhalli kuma an miƙa su zuwa majalisar dokoki domin gyara.

A cewarsa, dokokin da aka duba sun hada da Dokar Gandun Daji, Dokar Hana Kona Daji, Dokar Kiwon Dabbobi da Dokokin Tsafta.
Gwamna Namadi ya kara da cewa domin rage hadarin ambaliya da sarrafa ruwa, gwamnatin jihar ta sayi injina biyu masu iya aiki a ruwa da ƙasa domin kwance hanyoyin koguna da ciyawar Typha ta toshe.

“Baya ga wannan, gwamnati na aikin gina magudanan ruwa a wurare 32 daban-daban domin farfado da yankunan da ambaliya ta shafa. An kuma gina kilomita 130 na katanga a bakin rafuka domin rage ambaliya, kare gonaki da ƙarfafa ƙarfin gwiwar al’ummomin da ke cikin haɗari.”
Gwamnan ya yi gargaɗi mai ƙarfi ga masu sare itatuwa da masu yin gawayi da su daina, ko kuma su fuskanci fushin doka.

“Ina amfani da wannan dama in gargadi duk masu sare itatuwa ba bisa ka’ida ba, da masu yin gawayi da su daina. Kamar yadda muka ambata, mun duba dokokinmu na muhalli kuma mun tanadi hukunci mai tsauri ga duk wanda ya karya wadannan dokoki.”
Rediyon Najeriya ya bayyana cewa, Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim ne ya jagoranci dashen itatuwan da kuma raba irin shukar ga ƙananan hukumomi.
Wannan wani bangare ne na tsare-tsaren kare muhalli na jihar, wanda ya haɗa da samar da irin itatuwa mmiliyan biyu da rabi a duk shekara, wayar da kai, da kuma haɗin gwiwa da hukumomin ƙasa da na ƙetare.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
