Connect with us

Labarai

Tsofaffin Gwamnoni Sun Ziyarci Tinubu Tare Da Bashi Shawarwari Kan Matsalolin Tsaro

Published

on

Tsoffin gwamnoni da suka fara mulki a shekarar 1999, da ake kira “Class of ’99,” sun gana da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar Gwamnati da ke Abuja a ranar Juma’a, inda suka gabatar da shawarwari na aiki domin magance matsalolin tsaro, inganta tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi a fadin ƙasar.

Tawagar, ƙarƙashin jagorancin tsohon Gwamnan Jihar Edo, Lucky Igbinedion, ta haɗa da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), George Akume, da wasu tsoffin gwamnoni da suka yi mulki tare da Shugaba Tinubu lokacin da yake Gwamnan Jihar Lagos.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan ganawar da ta ɗauki fiye da awa guda, Igbinedion ya bayyana cewa ziyarar tasu na da nufin yin wata ganawa da ɗan ajinsu kuma su tattauna hanyoyin da za a ciyar da ƙasa gaba.

Mun zo ganin takwaranmu, wanda muka fara mulki tare a shekarar 1999, don tattauna batutuwan da ke da muhimmancii ga ƙasa. Mun tattauna kan batun tsaro, tattalin arziki, noma da samar da ayyukan yi. Shugaban ya nuna damuwa matuƙa kan waɗannan matsaloli, kuma ya karɓi shawarwarinmu da hannu biyu.” In ji shi.

Igbinedion ya jaddada cewa tsaro ya kamata ya kasance babban fifiko na gwamnati, domin ba za a samu ci gaba ba tare da zaman lafiya idan ba tsaro ba.

Game da batun ayyukan yi, tsohon gwamnan ya yi kira da a kafa masana’antu kanana (cottage industries) a kowace ƙaramar hukuma a matsayin hanyar dorewar rage rashin aikin yi da fatara.

In har za ka ba mutum tallafi yau, me zai faru gobe? Mun roƙi Shugaban Ƙasa da ya kafa ƙanana masana’antu a faɗin ƙasa domin mutane su samu ayyukan yi.” In ji shi.

Tawagar ta yaba wa Shugaba Tinubu bisa maraba da shawarwari masu amfani, inda suka ce Shugaban Ƙasar ya tabbatar musu da cewa zai yi la’akari da duk wani tunani mai amfani da zai ciyar da ƙasa gaba.

Shugaban Ƙasa ya tabbatar mana cewa ƙofofinsa a bude suke don tattaunawa da shawarwari masu amfani da za su inganta ƙasar nan.” In ji Igbinedion.

Wannan shi ne karo na biyu da tsoffin gwamnoni na  1999 ke ziyartar Shugaban Ƙasa Tinubu tun bayan hawansa mulki.

 

Bello Wakili

 

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai6 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara