Labarai
An Fara Zaman Jin Ra’ayoyin Jama’a Kan Sauya Kundin Tsarin Mulki A Kano
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril, ya kaddamar da zaman jin ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Yamma kan sauya kundin tsarin mulkin Najeriya a Kano.
Yayin gabatar da jawabinsa na bude taron, Sanata Barau ya yi maraba da manyan baki da suka halarci zaman, yana mai cewa: “Ina alfahari da zuwanku wannan zama na jin ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Yamma, wanda ya shafi kudurori da sabbin batutuwa dangane da gyaran kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya.”
Sanata Barau ya tunatar da cewa Majalisar Ƙasa ta riga ta amince da gyaran kundin tsarin mulki sau biyar, da aka fi sani da alteration acts na farko zuwa na biyar.
Ya jaddada cewa akwai muhimman batutuwa da ke buƙatar ƙarin matakin doka domin warware su. Cikin batutuwan da za a mayar da hankali a kansu akwai: Sauye-sauyen harkar zaɓe, gyara a fannin shari’a, gyaran kundin tsarin mulki, da gudanar da shari’u da tsare-tsarensu.
Sauran muhimman batutuwa sun haɗa da:Inganta ‘yancin ɗan adam, tabbatar da shigar mata a harkokin shugabanci, raba iko da haɓaka ci gaban ƙananan hukumomi, batutuwan tsaro da tsarin aikin ‘yan sanda, da sauransu.
Sanata Barau ya buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki da su ba da ra’ayoyi da shawarwari, yana mai cewa: “Mun buɗe ƙofofinmu ga dukkan ra’ayoyi. Kwamitin ya kuduri aniyar sauraron dukkanin bangarori yadda yakamata.” In ji shi.
Ya jaddada cewa shiga cikin irin wannan tsari na jama’a muhimmin al’amari ne ga makomar ƙasa.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jiha, Dr. Wali Sani, ya wakilta, ya jaddada bukatar haɗin kai, adalci da daidaito. A cewarsa: “ya zama mu yi ayyukan da za su haɗa ƙasa, su inganta adalci da daidaito, su kuma haɓaka ci gaba da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa gaba ɗaya.”
Abdullahi Jalaluddeen
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
