Labarai
Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Majalisar Abinci Mai Gina Jiki ta Jihar Jigawa
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da Majalisar Abinci Mai Gina Jiki ta Jihar Jigawa 774, inda ya tabbatar da kudurin gwamnatinsa na yaki da rashin abinci mai gina jiki da inganta yalwar abinci a fadin jihar.
An gudanar da kaddamarwar ne yayin ziyarar Mrs. Uju Rochas-Anwuka, mai bai wa Shugaban Kasa shawara ta musamman kan lafiya ( Karkashin Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa), wacce ta je Jigawa domin kaddamar da shirin Nutrition 774 da ke karkashin shirin sabunta kudurori na Renewed Hope Agenda.

Gwamna Namadi ya bayyana cewa Jigawa ta kasance gaba a yaki da matsalar, tare da kafa shiri na musamman da aka yi wa lakabi da Masaki tun a 2020 domin fadakar da al’umma a matakin ƙasa, wanda ya amfanar da sama da mutum miliyan 1 da dubu 300.
Ya kara da cewa gwamnati na ware Naira Miliyan 13 da rabi a kowane wata domin tallafa wa shirin na Masaki, da kuma Naira Miliyan 250 a shekara, don sayen abinci da magani tare da UNICEF, yayin da Majalisar Dokoki ke bayar da Naira Miliyan 300 a shekara.

Haka kuma, sama da mata 600 sun samu horo a shirin abincin yara na Tom Brown don samar da abinci mai gina jiki a gida tare da hadin gwiwar hukumar NAFDAC.
Gwamnan ya ce sabuwar majalisar za ta hada kai da ma’aikatun gwamnati wajen tsara da aiwatar da manufofin abinci mai gina jiki, tare da nufin sanya Jigawa ta zama ta farko da za ta cimma burin shirin gwamnatin tarayya naNutrition 774.

A jawabinta, Mrs Uju ta ce shirin na daga cikin manyan shirye-shiryen gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da nufin magance matsalar rashin abinci mai gina jiki a fadin kasar.
Usman Muhammad Zaria
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
