Labarai
A Shirye Nake Na Kare Nasarar Da Na Samu A Zabe – Tchiroma Bakary
Ɗan takarar jam’iyyar adawa a zaɓen shugaban ƙasar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary wanda ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen, ya shaida wa BBC cewa a shirye yake ya kare abin da ya bayyana “nasara ƙarara” da ya samu.
Yayin da al’ummar ƙasar ke ci gaba da dakon sakamakon zaɓen da za a bayyana a ranar Litinin mai zuwa, Bakary, wanda shi ma tsohon jami’in gwamnatin Paul Biya ne, ya ce zai amince ne kawai da sakamako na gaskiya.
Wannan kalami nasa dai zai ƙara rura wutar zaman ɗarɗar da ake yi a ƙasar ta yankin tsakiyar Afirka.
Tun daga farkon makon nan ne mutane, musamman magoya bayan Bakary suka riƙa fita kan tituna domin yin gangamin kira ga gwamnati ta tabbatar ta fitar da sakamako daidai da zaɓin al’umma.
A baya an tsara cewa za a bayyana sakamakon zaɓen ne ranar Alhamis, sai dai wata sanarwa daga gwamnati ta ce an ɗage bayyana sakamakon zuwa ranar Litinin ɗin mako mai zuwa.
Wasu alkalumman da kafofin yada labaran kasar suka ruwaito sun nuna cewa akwai yiyuwar shugaba Paul Biya ne zai zarce kan mulkinsa na shekara 43.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
