Labarai
Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Aikin Gina Hanyoyi Ba Naira Biliyan 81 A Malam Madori
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya jaddada kudirin gwamnatin sa na ci gaba da bunkasa hanyoyin sufuri a fadin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya kaddamar da wani muhimmin aikin gina hanyoyi a karamar hukumar Mallam Madori.
Yayin taron kaddamarwar, Gwamna Namadi ya bayyana cewa aikin yana cikin shirin “Gwamnati da Jama’a” wanda ke karfafa al’umma, rage matsalolin sufuri da kuma karfafa harkokin kasuwanci.

Ya ce shirin ya kunshi gina manyan hanyoyi guda shida a sassan jihar, masu tsawon kilomita 179 gaba daya, a kan kudin da ya haura Naira Biliyan 81.
Hanyoyin sun hada da Mallam Madori zuwa Gari Uku zuwa Kanya Babba zuwa Malorin Kasim, ta ratsa ta Abori Sumburtu, har zuwa Diginsa, mai tsawon kilomita talatin da hudu da rabi.

Sai kuma hanyar Arbus zuwa Girbobo zuwa Garin Bukar mai nisan kilomita talatin da uku da rabi.
Kazalika akwai hanyar Dundubus zuwa Yanjaji zuwa Wangara mai tsawon kimanin kilomita goma sha bakwai.

Akwai kuma hanyar Jahun zuwa Takalafiya zuwa Zareku zuwa Kafin Hausa da reshe daga Takalafiya zuwa Dangyatum mai kilomita talatin da takwas.
Da hanyar Kukayasku zuwa Malamaba zuwa Katuka zuwa Garin Kwalandi mai nisan kilomita talatin da hudu da rabi.

Sai cikon ta shidda wacce ta tashi daga Farun Daba zuwa Maitsani zuwa Baauzini zuwa Kafin Chiroma zuwa Gallu Babba zuwa Gallu Karama ta kai ga Karkarna Bypass mai nisan kilomita goma sha uku.
Gwamnan ya bayyana cewa tuni an yi kashi 35 cikin 100 aikin, yana mai fatan cewa za a gama shi cikin shekara guda, kafin wa’adin watanni 18.
Ya tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da baiwa ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, noma da samar da ayyukan yi muhimmanci a karkashin Manufofi 12 na Gwamnati don Cigaban Jigawa.

Ya kuma gode wa Gwamnatin Tarayya a karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa tallafi da daidaiton manufofi.
A yayin ziyarar, Gwamna Namadi ya kuma kaddamar da sabon masallaci da aka gina a Garin Gabas, wanda shugaban karamar hukuma ya tallafa wajen ginawa.
Shugabannin al’umma sun mika wa Gwamnan kundin bukatun jama’a a matsayin wani bangare na tsarin mulkin jin ra’ayin al’umma.
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
