Connect with us

Ilimi

Gwamna Namadi Tare Da Hadin Gwiwar Kasar Qatar Sun Samar Da Cibiyar Bunkasa Ilimi A Jigawa

Published

on

Gwamna Mallam Umar Namadi ya kaddamar da Cibiyar Al’amuran  Addinin Musulunci a kauyen Babbar Riga dake karamar hukumar Malam-Madori a jihar Jigawa.

Cibiyar wacce aka ginata tare da  hadin gwiwar wata kungiyar Agaji ta kasar Qatar mai zaman kanta da kuma gwamnatin jihar Jigawa, an tsara shi ta ne  domin kawo sauyi ga al’umma ta kyautata rayuwarsu, da samar da ingantaccen ilimi.

Sabuwar cibiyar da aka kaddamar ta kunshi rukunin gidaje, da ginin makaranta na zamani, da masallaci, wadanda za su samar da yanayi mai kyau na koyo da ci gaban al’umma.

Wannan shiri ya jaddada kudirin gwamnatin jihar Jigawa na bunkasa ilimi da inganta rayuwar al’umma.

A yayin bikin, Gwamna Namadi ya yabawa kungiyar Qatar Charity bisa sadaukarwar da ta yi, sannan ya bukaci a ci gaba da hada kai don fadada irin wadannan ayyuka a fadin jihar Jigawa.

Ya sanar da cewa hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar (SUBEB) za ta kula da wurin domin tabbatar da kulawar da ta dace, tare da samar da  malamai da sauran kayayyakin aiki a makarantar.

 

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan jihar Jigawa, Hamisu Mohammed Gumel ya fitar, ya ce bikin kaddamarwar ya samu halartar manyan baki da suka hada da jakadan Qatar a Najeriya, Ali Bin Ghanem Al-Hajri; da Daraktan kungiyar agaji ta Qatar, Hamdi Abdou.

 

Sauran sun hada da Darakta-Janar na Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA), Kashifu Abdullahi; da  Sarkin Hadejia, Alhaji Adamu Abubakar Maje; da sauran fitattun shugabanni da sauran al’umma.

Kungiyar Qatar Charity ta mikawa gwamnatin jihar Jigawa ginin a hukumance, inda al’ummar yankin suka fara amfani da ita.

Mista Hamdi Abdou, daraktan kungiyar agaji na kasar, ya yabawa Gwamna Namadi bisa hangen nesa, tare da yin alkawarin ci gaba da kawo dauki a jihar Jigawa a wannan shekarar  ta 2025.

Wannan aiki na nuni da  cika alkawarin da Qatar Charity ta yi a lokacin da Gwamna Namadi ya ziyarci ofishinsu na Abuja a shekarar da ta gabata.

Da wannan hadin gwiwa, jihar Jigawa na ci gaba da kafa tarihi na hadin gwiwa mai ma’ana da nufin magance kalubalen ilimi da gidaje, da samar da ci gaba mai dorewa ga al’ummarta.

 

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai9 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara