Labarai
Ana Sa-In-Sa Tsakanin NUJ Da Tsohon Shugaban NLC A Jihar Kabi
Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ reshen jihar Kebbi, ta yi watsi da ikirarin da tsohon shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), AbdulWaheed Ibrahim Umar ya yi na cewa kafafen yada labarai na rashin bayar da rahoton irin nasarorin da al’ummar Kebbi da gwamnatin jihar suka samu.
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Alhaji Kabiru Wurma ya raba wa manema labarai a Birnin Kebbi, ya bayyana kalaman Umar a matsayin yaudara da kuma wani yunkuri na burge Gwamna Nasir Idris a yayin jawabin da ya yi a kungiyar NLC a jihar.
Wurma ya ce, “Mun yi matukar ba mu mamaki a lokacin da Kwamared Umar a lokacin da yake fadar shugaban kasa ya yi ikirarin cewa ya zagaya jihar domin tabbatar da nasarorin da Gwamna Idris ya samu cikin shekaru uku kacal.
Shugaban kungiyar ta NUJ ya kara jaddada irin goyon bayan da Gwamna Idris ya samu daga kafafen yada labarai, inda ya ce, “Babu wani gwamna a Najeriya da ya taba samun rahotannin da ake samu daga ‘yan jarida da kungiyoyin yada labarai kamar Gwamna Nasir Idris.
Ya kuma tunatar da cewa, a ziyarar da shugaban NLC na yanzu, Joe Ajero ya kai jihar Kebbi a ranar 23 ga Oktoba, 2024, ya yaba wa gwamnan, inda ya ce, “Babu ranar da labarai masu kyau ba sa fitowa daga jihar Kebbi.
Shugaban kungiyar ya kuma yi tambaya kan dalilin da ya sa tsohon shugaban NLC din zai yi ikirarin a kan al’amuran da ba shi da masaniya a kai, yana mai cewa babu wani aiki daya da ‘yan jarida ba su kama ko su yi aiki ba a jihar.
REL/ SANI DUTSINMA
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
