Connect with us

Labarai

An Kama Wata Budurwa Da Ke Jagorantar Masu Satar Waya A Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sanda a  jihar Kano ta tarwatsa wata kungiya kalkashin  jagorancin wata yarinya mai suna Shamsiyya Adamu, da ke da hannu wajen satar wayar hannu, lamarin da ya kai ga kama biyar daga cikinsu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sandan Bompai kano.

Ya tabbatar da cewa an kama Shamsiyya mai shekaru 19 ne a ranar 21 ga watan Disamban 2024, biyo bayan rahotannin satar wayoyin hannu a yankin Unguwa Uku, inda aka rika  samun  korafe-korafe da dama daga mazauna birnin Kano kan wata budurwa da ake zargin tana satar wayoyin hannu a gidaje.

Ya kara da cewa, bincike ya nuna cewa Shamsiyya, tare da taimakon ’yan damfara da masu aikata laifuka ta yanar gizo, suna kai hari kan matan aure.

Binciken da aka yi kan sace-sacen wayoyin salula,  ya yi sanadiyyar  kama Shamsiyya, inda aka  gano cewa baya ga satar wayoyi, kungiyar tana da hannu  wajen  yin amfani da bayanan banki da ake sata wajen fitar da kudi daga asusun wadanda abin ya shafa,” in ji SP Kiyawa.

Kiyawa ya kara da cewa, abubuwan da kungiyar ke yi sun  hada da yaudarar matan aure domin  sace musu wayoyinsu, inda wani mai  keken napep ke jigilar Shamsiyya zuwa wurare daban-daban, yayin da masu laifin ta yanar gizo sun yi amfani da bayanan bankin da aka sata don tara kudade daga asusun ajiyar banki na jama’a.

Wadanda ake zargin sun hada da Shamsiyya Adamu, mai shekaru 19, wacce ita ce shugaba, da Idris Yusuf, dan shekara 23, da Al’asan Dahiru, dan shekara 24, da Abdulmajid Haruna, dan shekara 27, wanda ya sayi wayoyin da aka sace da Salim Auwalu, dan shekara 21 da ya yi amfani da fasahar yanar gizo wajen satar kudi.

An kwato wayoyin hannu guda shida da aka sace daga hannun Abdulmajid.

Kiyawa ya kara da cewa kawo yanzu, masu korafi 30 da suka hada da mata 29 da namiji daya ne suka kai rahoton sace musu wayoyinsu.

Shamsiyya ta amsa laifin satar wayoyi a lokuta daban-daban a cikin shekarar da ta gabata.

 

Abdullahi Jalaluddeen­

Labarai

Labarai15 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai2 days ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai2 days ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara