Labarai
Kasar Congo Ta Yankewa Sojoji 13 Hukuncin Kisa Bisa Saɓa Dokar Aiki
Wata Kotu a Jamhuriyyar Congo ta zartas da hukuncin kisa kan wasu Sojoji 13 bayan samunsu da laifuka masu alaƙa da kisan kai da sace sacen dukiyoyin jama’a da kuma ragwantaka a fagen daga, yayin mamayar da mayaƙan M23 suka yi wa yankin da suke bai wa kariya.
Yayin zaman kotun na jiya Laraba ne ta zartas da hukuncin kisan kan Sojojin 13, bayan abin kunyar da suka aikata a yankin Lubero na gabashin lardin Kivu, wanda ta ce ya saɓawa horarwar Soji a ƙasar mai fama da rikici na tsawon shekaru, ciki har da hare-haren M23 da ke cika shekaru 3 da farowa.
Akalla sojoji 24 ne suka gurfana gaban kotu yayin hukuncin na jiya, Baya ga wadanda aka yanke wa hukuncin kisa, hudu sun samu hukuncin zaman shekaru 2 zuwa 10 a gidan yari, an kuma wanke wasu shida, sannan an ɗage karar daya don ci gaba da bincike.
Mai gabatar da ƙara a kotun Kabala Kabundi, ya bayyanawa kamfanin dillacin labaru na Reuters cewa an gudanar da shari’ar ce domin tabbatar da ɗorewar ɗa’a da aminci a tsakanin al’umar kasar da kuma dakarun sojin kasar.
A yayin shari’ar dai dukkanin wadanda aka gurfanar sun amsa laifinsu, inda da kotun ta baiwa mutum biyar daga cikinsu kwanaki biyar na su ɗaukaka ƙara in sun buƙaci hakan.
RFI
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
