Labarai
Iyalan Waɗanda Aka Kashe Yayin Zanga-zangar Bangladesh Sun Yi Maraba Da hukuncin Kisan Tsohuwar Firaminstar
Iyalai da ‘yan uwan wadanda aka kashe a lokacin zanga-zangar da ta kawo karshen gwamnatin tsohuwar Firaminstar Bangaledash Sheikh Hasina a bara, sun yi maraba da hukuncin kisa da wata kotun birnin Dhaka ta yanke mata.
An samu Sheikh Hasina da laifin cin zarafin bil adama tare da ba ‘yan sanda umurnin kashe masu zanga-zanga, inda aka yanke mata hukuncin a bayan idonta.
Gwamnatin Bangaledash ta bukaci Indiya da ta tasa keyar Hasina da ke gudun hijira a can domin ta fuskanci hukuncin.
Wakiliyar BBC ta ce Hukumomin Indiya na cewa suna ci gaba da bibiyar lamarin tsakanin Sheikh Hasina da mahukuntan Bangaledash kuma hakan na nufin Indiya na neman wata hanyar diflomasiyya akan lamarin.
BBC
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
