Labarai
Shugabar Tanzania ta Naɗa ‘Yarta da Surikinta Ministoci a Ƙasar
Shugabar ƙasar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta fitar da sunayen sababbin ministocin ƙasar, inda ta sanar da ƙirƙirar sabuwar ma’aikatar matasa, wanda hakan ya ƙara yawan ma’aikatun ƙasar daga 26 zuwa 27 a sabuwar gwamnatin.
Daga cikin ministocin akwai sababbin fuskoki, da tsofaffin ƴan siyasar ƙasar, ciki har da tsofaffin ministoci bakwai, sannan ba ta mayar da tsohon mataimakin firaministan ƙasar kuma ministan makamashi, Dotto Biteko da tsohon shugaban majalisar ƙasar, Tulia Ackson ba.
Sai dai hankali ya fi karkata ne kan naɗin ƴar shugabar ƙasar, Wanu Hafidh a matsayin mataimakiyar ministar ilimi, sannan ta naɗa surikinta, Mohamed Mchegerwa a matsayin ministan lafiya a cikin sababbin ministocin.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan shugabar ƙasar ta kafa kwamitin bincike domin gano musabbin zanga-zangar bayan zaɓe da aka yi a ƙasar.
Jam’iyyun hamayya da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam sun zargi jami’an tsaron ƙasar da kashe ɗaruruwan mutane, sannan suka ɓoye gawarwakinsu.
Sai dai har zuwa yanzu hukumomin ƙasar ba su fitar da alƙaluman waɗanda suka mutu ba.
Samia Suluhu Hassan dai ta lashe zaɓen ƙasar ne da kashi 98 na ƙuri’ar kasar.
bbc
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
