Labarai
An Kaddamar Da Kwamatin Inganta Ayyukan Samar Da Jini Ga Marasa Lafiya A Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da kwamitin kwararru na jihar kan batun karin jini domin magance gibi da kalubalen da ke tattare da ayyukan karin jini.
Babban manufar kwamitin ita ce tabbatar da yin ƙarin lafiyayyen jini fa marasa lafiya a jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya kaddamar da kwamitin, inda ya bayyana cewa kafa kwamitin na da matukar muhimmanci wajen kare kamuwa da wata cuta sakamakon karin jini.
Ya kuma jaddada cewa an zabi ‘yan kwamitin ne bisa cancanta da kwarewarsu.
Kwamitin yana da alhakin samar da kwararru masana kula da lafiyar jini, da masu bada shawarwari kan lamarin, da haɗin gwiwa tare da masu ruwa da tsaki don haɓaka ayyukan ƙarin jini.
Kwamitin ya ƙunshi wakilai daga cibiyoyin kiwon lafiya daban-daban, waɗanda suka haɗa da Hukumar Kula da Asibitoci, da Hukumar Kula da Cibiyoyin Kiwon Lafiya Masu Zaman Kansu, da Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko, da Hukumar Samar da Magunguna.
Hakavkuma akwai wakilai daga cibiyoyin ilimi, kamar Jami’ar Bayero Kano da Asibitin koyarwa na Aminu Kano.
Sakatariyar kwamitin, Dokta Hauwa Ibrahim, kwararra kan al’amuran da suka shafijini, za ta kasance mai bada shawarwari ga kwamitin.
Kwamitin yana da ‘yancin yin haɗin gwiwa tare da ƙarin masu ruwa da tsaki kamar yadda ake buƙata.
Kaddamar da kwamatin wani muhimmin mataki ne na inganta ayyukan samar da jini a jihar Kano, tare da tabbatar da tsaro da jin dadin majinyatan da aka yi musu karin jini.
Daga Khadija Aliyu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
