Labarai
An Gargadi Al’ummar Jihar Kwara Game Da Illar Zubar Da Shara A Tituna
An gargadi mazauna jihar Kwara kan zubar da shara ba bisa ka’ida ba, don hana barkewar cututtuka.
Kwamishinar Muhalli ta jihar, Hajiya Nafisat Musa-Buge, ta yi wannan gargadin a lokacin da ta karbi rahoton Kwamiti na musamman na Ma’aikatan Lafiyar Muhalli, bayan wani aikin da ya gudanar a Ilori.
Ta ce jihar ta yi fice a tsakanin takwarorinta, saboda kokarin da take yi na kawar da zubar da shara barkatai da kuma dorewar yanayi mai tsafta.
Hajiya Nafisat Musa-Buge ta bayyana cewa wadanda aka kama bisa karya dokokin muhalli za a gurfanar da su a gaban Kotu domin su fuskanci hukunci.
Ta bayyana kwarin gwiwar cewa goyon bayan da ma’aikatar ke samu daga gwamnatin jihar zai taimaka wajen dorewar yanayi mai tsafta ga kowa.
Kwamishinar ta kuma yabawa jami’an hukumar kula da muhalli bisa kulawar da suke yi da kuma jajircewarsu wajen kawar da zubar da shara ba bisa ka’ida ba, a jihar.
Ta yi kira ga jama’a da su bai wa gwamnati mai ci goyon baya, a kokarinta na tabbatar da tsaftar muhalli.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
