Ilimi
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Samar Da Sufuri Kyauta Ga Dalibai
Gwamnatin jihar Kwara ta yi tanadin sufuri kyauta ga daliban da suke komawa makaranta bayan hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara domin saukaka musu tsadar sufuri.
Kwamishinar kasuwanci, kirkire-kirkire da fasaha na jihar, Damilola Adelodun ne ta bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Ilori.
Ta ce an tanadi tallafin sufurin ne don daukar nauyin dukkan daliban jami’ar gwamnatin tarayya da ke Ilori wato UNILORIN, da kuma na jami’ar jihar wato KWASU.
Damilola ta bayyana cewa an samar motocin bas bas din a makarantar Queen Elizabeth ta Taiwo, da kuma dandalin Soludero dake ofishin gidan waya, a Ilorin.
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta himmatu wajen tallafawa harkokin ilimi ga al’ummarta.
Damilola ta shawarci daliban da suka dawo makaranta da su yi amfani da damar da suka samu wajen neman ilimi tare da bin ka’idojin karatu.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
