Labarai
Jami’an ‘Yan Sanda 272 Sun Sami Karin Girma A Kano
Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kano, Salman Dogo Garbaya ja hankalin jami’an rundunar jihar su 272 da suka sami karin girma da su kasance masu kishin kasa, da kwazo da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.
CP Salman Dogo Garba ne ya bayyana haka ne a lokacin da yake bai wa jami’an shaidar karin a hedikwatar ‘yan sanda da ke Bompai, a Kano.
Ya bukace su da su sauke nauyin da aka dora musu, ta hanyar kula da hakkin al’umma da kuma kare dukiyoyinsu.
“Sabbin mukamanku suna tattare ne da sabbin ayyuka da ke bukatar kishin kasa, da sadaukarwa wajen yi wa al’umma hidima.” Inji Garba.
“Ina so in tunatar da ku cewa, wannan wani kalubale ne a gare ku. Yayin da kuke samun karin girma, ayyukanku ne suke karuwa. Ina yi muku fatan samun nasara a yayin ayyukanku.”
Kwamishinan ya ce al’ummar Kano da ma ‘yan Najeriya na sa ran abubuwa da dama daga gare su, inda ya bukaci jami’an da aka kara musu girma da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu bisa tsoron Allah.
Ya ce jami’an da aka kara wa girma sun hada da manyan Sufetan ‘yan sanda 4 da suka sami mataimakin kwamishinan ‘yan sanda AC, sai Sufetan ‘yan sanda 50 da suka sami mukamin babban Sufetan ‘yan sanda, da mataimakan Sufurtandan ‘yan sanda 32 da suka zama Supretendad, da kuma jami’ai 182 da suka zama mataimakan Sufurtandan ‘yan sanda.
Iyalan jami’an da suka sami karin girman na daga cikin manyan bakin da suka halarci taron.
Abdullahi Jalaluddeen
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
