Labarai
An Sami Kwararar Ruwa Fiye Da Kima A Gonakin Shinkafa A Jihar Kwara
Gwamnatin Jihar Kwara ta bayyana damuwarta kan kwararar ruwa fiye da kima a gonakin shinkafa da dama a Shonga, da ke karamar hukumar Edu ta jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Rafiu Ajakaye ya fitar, ya ce Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya kafa kwamitin da zai binciki musabbabin ambaliyar.
A cewarsa ana sa ran kwamitin zai ziyarci yankunan da lamarin ya shafa domin gudanar da bincike.
Sanarwar ta ce kwamitin zai kai ziyarar jaje ga Sarkin Shonga Dr. Haliru Yahyah da wadanda abin ya shafa a cikin al’umma.
Mambobin kwamitin da mataimakiyar shugaban ma’aikatan jihar, Gimbiya Bukola Babalola za ta jagoranta, sun hada da kwamishinan ayyukan gona, Mrs Oloruntoyosi Thomas, da kwamishinan muhalli, Hajiya Nafisat Musa Buge; da mai ba da shawara na musamman kan ayyuka na musamman; da tsaro ga Gwamna, Alhaji Muhyideen Aliu, da sauransu.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
