Connect with us

Ilimi

UNICEF Ya Kara Jan Hankalin Gwamnatin Najeriya Game Da Ilimin ‘Ya’ya Mata

Published

on

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su kara himma wajen yara mata na samun damar yin karatu.

Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah, ne ya yi wannan kiran a Kano a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta 2025.

Ya kara da cewa alkaluma sun nuna cewa ‘yan mata miliyan 7 da 600 ba sa zuwa makaranta, inda shiyyar Arewa maso Yamma da arewa maso gabas ke da kashi 48 cikin 100 na adadin.

Ya danganta wannan kididdigar da abubuwan da suka hada da talauci da ka’idojin zamantakewa da nuna wariyar jinsi, wadanda ke dakile bai wa ‘ya’ya mata damar samun ilimi.

A lokacin da yake gabatar da bitar ayyukan UNICEF na inganta karatun yara mata da kuma ci gaba da karatu, shugaban ofishin kula da kananan yara na jihar Kano, Rahama Mohammed Farah, ya ce asusun ya samu  hadin gwiwa da gwamnati da al’umma wajen magance matsalolin.

Ya ce UNICEF ta kuma yi amfani da tallafin kudi da sauran abubuwan karfafa gwiwa don karfafawa iyaye gwiwa, su yi rajistar ‘ya’yansu mata da tabbatar da ganin sun ci gaba da zuwa makaranta.

Ya yi bayanin cewa, “UNICEF ya yi kokari matuka a wannan fanni, ciki har da bayar da kudade domin karfafa musu gwiwa wajen tura ‘ya’yansu mata zuwa makaranta tare da tallafa musu zuwa matakin sakandare”.

Ya yi bayanin yadda asusun ya ke inganta fasahar rubutu da karatun ‘ya’ya mata ta hanyar cibiyoyin karatun ‘yan mata don ‘yan mata (G4G), inda kimanin ‘yan mata da ke zuwa makaranta miliyan 2 da 600 su ke samun ilimi ta hanyoyin sadarwa da suka hada da rediyo da talabijin a hakin yanzu.

UNICEF ya kuma inganta kwazon malamai don ilmantar da ‘ya’ya mata, tare da kara yawan malamai a makarantun firamare 42,000“, inji Farah.

Ya yi bayanin cewa UNICEF ya kuma gina tare da gyara wuraren tsaftar ruwa a makarantu 33 a fadin jihohin Kano da Jigawa,  wadanda ‘yan mata 19,622 ke amfani da su.

Ya ce asusun yana kuma  aiki tare da masu tsara manufofi a fannin ilimi don tabbatar da ingantacciyar kariya ga yara da ayyukan makaranta ga yara mata, yayin da kuma yana inganta kwazon malamai  da za su  jagoranci  yara mata.

Taron manema labaran ya samu halartar ‘yan jaridu  daga jihohin Kano,  da Jigawa da Katsina.

Usman Mohammed da Isma’il Adamu

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara