Ilimi
An Bukaci Musulmai Su Ware Dukiya Don Ayyukan Ci Gaban Al’umma – Cibiyar Al-Furqa
An bukaci Al ummar musulmi da su cire wani kaso daga cikin dukiyarsu wajen gudanar da wasu ayyukan cigaba da habbakasu don cigaban al umma.
Shugaban cibiyar ayyukan Alheri ta Al furqan dake Kano , Muhammad Abubakar ya bayyana bukatar hakan a lokacin wani taro na wayar da Kai kan wakafi da tasirinsa wajen cigaban al umma a da ya gudana a dakin taro na Jama atu Nasril Islam dake Jos, a jihar Plateau.
Dr Abubakar yace , Al ummomi na bukatan hazikan mutane da zasu zuba jari da za a dunga amfani da kudaden wajen tafiyar da ayyukan tallafawa al umma.
Ya bukaci Masu hannu da shuni da su dinga koyar da yayansu ayyukan taimakon al umma don dawwamar ayyukan Alheri bayan .
Hakalika, ya bayyana Karin samun yawaitan ayyukan Alheri da aka waresu na taimakon al umma da suka hada da makarantu , wurin koyon sana o e, da daukan nauyin gajiyayyu da sauransu da suke taimakawa wajen cigaban al umma.

Da yake nasa jawabin , Shugaban cibiyar bincike da tattara bayanai ta Mahanga research centre , ,Limamin massallacin sultan Bello, Dr Suleiman Muhammad Adam, yace ayyukan alheri da aka gudanar ta hanyar wakafi ,sun taimaka wajen kawo sauye sauye a rayuwan alumma da dama da suka hada da rayuwar marayu, marasa galihu ta hanyar daukan nauyin karatunsu da lafiyarsu.
Limamin na sultan bello ya bukaci kwararru kan harkar ilimin wakafi , da sukara wayar da kan Yan Kasarnan wajen fahimtar muhimmancin sa da gudunmawar da yake bayarwa wajen cigaban rayuwar al umma.
COV/ABUBAKAR ADAM
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
