Connect with us

Labarai

Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Ta Fara Biyan Rarar Kudade Ga Alhazan 2023

Published

on

 

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta fara biyan Naira 61,080 ga mahajjata 6,239 kowannensu,  da suka yi aikin Hajji daga jihar a shekarar 2023.

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Yunusa Mohammed Abdullahi ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa kowane mahajjaci zai karbi kudi naira 61,080, kuma za a shigar da wadannan kudade kai tsaye cikin asusun ajiyar maniyyatan da abin ya shafa.

Hukumar ta karbi wadannan kudaden ne daga hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON)”. Inji sanarwar.

NAHCON ta bayyana  cewa an mayar da kudaden ne sakamakon katsewar wutar lantarki a lokacin da Alhazai suka yi zaman Muna, lamarin da ya shafi na’urorin sanyaya daki, da kuma kawo cikas ga mahajjata”.

“Za mu yi duk mai yiwuwa don tabbatar da ganin an biya mahajjatan ta asusun  bankinsu don gujewa matsala,” inji Shugaban Hukumar, Malam Salihu S. Abubakar, a wani taro da jami’an  Alhazai na kananan hukumomin.

Sanarwar ta yi kira ga Alhazan da abin ya shafa da har yanzu ba su mika bayanansu ba da su tuntubi jami’an karamar hukumarsu domin a tantance su .

Abubuwan da ake buƙata don tantancewar sun haɗa da fasfo na tafiya da bayanan asusun banki.

Shugaban Hukumar, Malam Salihu S. Abubakar, ya bukaci jami’an hukumar da su tabbatar da bin ka’idoji bisa  gaskiya da  amana.

 

Adamu Yusuf

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara