Labarai
An Bayar Da Horo Na Musamman Ga Mahauta A Jihar Kwara
An horar da mahauta sama da 300 a fadin kananan hukumomi 16 na jihar Kwara kan yadda ake sarrafa nama da tsaftar muhalli don kare yaduwar cututtuka.
Da yake jawabi a wajen taron horaswar da hukumar da ke kula da kiwon dabbobi ta jihar Kwara tare da hadin gwiwar ma’aikatar noma da raya karkara da kuma kungiyar Bolaniks suka shirya, Gwamna AbdulRahman AbdulRazq ya ce horon wani bangare ne na kokarin gwamnatin jihar na tabbatar da lafiyar abinci da kuma kare yaduwar cututtukan dabbobi.
Gwamnan wanda kwamishinan aikin gona da raya karkara ta jihar Misis Oloruntoyosi Thomas ta wakilta, ya ce shirin zai kuma bayar da kayayyakin kariya wato PPE kimanin dubu uku ga masu gudanar da kasuwancin kiwo da mahauta a jihar.

AbdulRazaq ya bayyana cewa horon zai baiwa masu kiwon dabbobi damar samun kwarewa kan inganta lafiyar dabbar Dabbobinsu.
Ya yi nuni da cewa, gwamnatin jihar ta samar da shirin da zai kwadaitar da jama’a su fara noma a muhallansu domin rage tsadar kayan abinci.
A jawabinsa Daraktan Kiwon Lafiyar Jama’a na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kwara, Dokta Oluwatosin Fakayode ya ce shirin an yi shi ne don tabbatar da lafiya ga mutane da dabbobi.

A nata jawabin, daraktan kula da lafiyar al’umma da cututtuka ta sashen dabbobi a ma’aikatar noma da raya karkara ta jihar Kwara, Dr.Idiat Omolola-Amin ta ce shirin an yi shi ne domin tabbatar da tsaftar muhalli a mahauta daban-daban da ke fadin jihar.
Ta ce ma’aikatar za ta ci gaba da wayar da kan jama’a kan bukatar sayen nama a kasuwannin da gwamnati ta amince da su.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
