Labarai
Al’ummar Jigawa Sun Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Shirin Ciyarwa Na Watan Ramadan
Al’ummomin Jihar Jigawa na ci gaba da nuna jin dadinsu dangane da bullo da ciniyoyin yin bude baki a watan Ramadan.
Wasu daga cikinsu da Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya zanta da su, da suka fito daga kananan hukumomin Dutse da Ringim da Hadejia da Gumel, da kuma Kazaure, sun bayyana cewar wannan hangen nesa da Gwamnan yayi zai matukar kawo masu sauki a wannan yanayi da ake ciki na hauhawar farashin kayan abinci.

Mallam Ali Bashir Kazaure da Dahiru Dutse sun nuna gamsuwa bisa cibiyoyin da gwamnatin jihar ta kafa domin ciyar da al’umma abincin bude baki.
Suma da suke tofa albarkacin bakin su, Malama Hansatu Sidi dake karamar hukumar Ringim da Talatu Abashe dake karamar hukumar Hadejia sun bayyana godiyarsu ga Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi bisa wannan tallafin kayayyakin abinci da aka fara kaddamarwa na rabawa al’ummar jihar.

Suna mai cewar shakka babu, suna samun tagomashi daga Gwamnati bisa tallafi da ake raba wa al’umma, musamman a kauyaku masu wahalar shiga.
Sai dai kuma, Malam Nura Usman Gumel yayi kira ga masu hannu da shuni da kungiyoyin da ba na gwamnati ba, da su taimakawa mutane da abinci a wannan watan na ramadan mai albarka.

Ya kuma bukaci al’umma da su rika tunawa gami da taimakawa marayu da abinci da suturu, domin samun lada a wajen Allah SWT.
Wakilinmu ya bamu rahoton cewar, kayayyakin da aka raba sun hada da buhunan shinkafa da masara dubu dari uku da katan din taliya dubu dari daya.

Kazalika, Gwamnatin jihar na sa ran mutane dubu dari daya da saba’in da tara da da dari bakwai ne za su amfana da tallafin ciyarwar a kowace rana na tsawon wata guda a jihar.
Usman Mohammed Zaria
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
