Kasuwanci
Al’ummar Jigawa Sun Bukaci Gwamnati Ta Yi Koyi Da Shirin NG-CARES Wajen Tallafawa Mabukata
Al’ummar Jihar Jigawa sun yi kira ga Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi da ya yi amfani da kyawawan tsarin da gaskiya wajen zabar wadanda za su ci gajiyar shirye-shiryen bada tallafin karfafa sana’o’i.

Sun kuma bukaci gwamnatin jihar da ta yi amfani da tsarin bayar da tallafin karfafa al’umma ma gwamnatin tarayya na (FADAMA) a dukkan shirye shiryenta ta bada tallafi, domin ganin al’ummar jihar sun ci gajiyar ayyukan gwamnati.

Wani shugaban al’ummar yankin Walewale a karamar hukumar Garki, Malam Haruna Abdullahi, ya ce, hanyar da shirin FADAMA na gwamnatin tarayya ya yi amfani da ita ya tabbatar da cewa tallafin ya isa ga masu bukata.

A cewarsa, tsarin ya kawar da son zuciya da siyasa, wanda hakan ya yi tasiri matuka ga al’umma.
“Mun ga yadda shirin FADAMA kkarkashin shirin gwamnatin tarayya na G-CARES ya samu damar tallafawa manoma na hakika da sauran mutanen da suka cancanta, idan aka yi amfani da wannan tsari a duk wasu tsare-tsare na karfafawa, zai kawo ci gaba na hakika a jihar Jigawa.”

Wani mazaunin garin, Usman Alhaji na Arbun a karamar hukumar Auyo, ya kara da cewa daukar tsarin zaben wadanda suka cancanta zai kara wa gwamnatin jihar kima a idon jama’a.

Sun bukaci Gwamna Namadi da ya yi amfani da wannan tsari ga sauran shirye-shiryen karfafawa a jihar, tare da tabbatar da cewa tallafin gwamnati na isa ga wadanda suka fi bukata.
Shi ma da yake jawabi, shugaban kwamitin riko na shirin FADAMA CARES, Dakta Saifullahi Umar ya bayyana cewa, shirin na NG-CARES an tsara shi ne domin dakile matsin tattalin arzikin da annobar Corona
. ta haifar.
Dakta Saifullahi ya ce, abu na 2 wanda aka aiwatar ta hanyar shirin FADAMA, yana mai da hankali ne kan tallafin noma da inganta rayuwa, ta hanyar yin amfani da kyakkyawan tsari wajen zabo wadanda suka dace su ci gajiyar shirin.
Usman Muhammad Zaria
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
