Labarai
Hukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Kammala Shirin Rigakafi ga Maniyyatan Bana
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta kammala tanadin katin shaidar rigakafin cututtuka ga dukkan maniyyatan aikin Hajjin shekarar 2026.
Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse.
Ya bayyana cewa katin rigakafin wajibi ne ga dukkan maniyyatan da za su tafi ƙasar Saudiyya domin aikin Hajji.

Alhaji Labbo wanda ya bayyana cewa jihar Jigawa na daga cikin jihohin da suka fara kammala shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2026, ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da tarukan wayar da kai da horar da maniyyata a kowace rana a dukkan ƙananan hukumomi 27 na jihar a cibiyoyin da aka tanadar
Ya ce nan ba da jimawa ba hukumar za ta fara raba yunifom da sauran kayayyakin tafiya ga maniyyatan 2026.

Labbo ya yaba wa ma’aikatan hukumar bisa ƙwazon su da haɗin kai wajen gudanar da ayyukansu.
Haka kuma, shugaban hukumar ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa ci gaba da ba su goyon baya da haɗin kai.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
