Labarai
Sarkin Musulmi Ya Ayyana Ranar Juma’a 1 ga Watan Shawwal
Daga Nasir Malali
Mai Martaba Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ayyana ranar Juma’a, 20 ga watan Maris a matsayin ranar 1 ga Shawwal na shekarar 1447 bayan hijira, wanda hakan ke nuna ƙarshen azumin Ramadan na wannan shekara.
A cikin wata sanarwa da shugaban Kwamitin Shawarwari kan Harkokin Addini na Majalisar Masarautar Sakkwato, Sambo Wali Junaidu ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa Majalisar Masarautar tare da Kwamitin Duba Wata na Ƙasa ba su samu wani rahoto da ke tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal ba a yau Laraba, 18 ga watan Maris na 2026, wanda ya yi daidai da 29 ga watan Ramadan na shekarar 1447 bayan hijira.
Sanarwar ta ƙara da cewa ranar Juma’a, 20 ga watan Maris, wadda ta yi daidai da 1 ga Shawwal, ita ce ranar gudanar da Sallar Idi da kuma bikin Eid-el-Fitr.
Mai Martaba Sarkin Musulmin ya taya al’ummar Musulmin Najeriya murna, tare da fatan alkairi.
-
Labarai3 days agoGwamnatin Zamfara Ta Amince da Biyan Albashin Watan Maris Gabanin Bukukuwan Karamar Sallah
-
Labarai6 days agoKwastam Ta Kama Kayayyakin Fasa Kwauri Na Naira Miliyan 478 A Kwara
-
Labarai6 days agoJami’ar Bayero Kano Ta Yi Martani Kan Zargin Damfarar Dalibi
-
Labarai6 days agoAn Yi Wa Jami’an FRSC A Jos Gwajin Idanu Kyauta Domin Ranar Glaucoma Ta Duniya
-
Labarai2 days agoGidauniyar NASARA Ta Raba Kayayyakin Ramadan da na Sallah ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoMatashi Mai Digiri Na Farko Na Sayar Da Ruwan Leda A Taraba
-
Labarai3 days ago‘Yan Sanda Sun Bankado Maboyar Masu Garkuwa
-
Labarai3 days agoJIBWIS Ta Bukaci Gwamna Bago Ya Gaggauta Sanya Hannu Kan Dokar Hisbah
