Labarai
Tinubu Ya Nada Ibrahim Masari a Matsayin Mai Ba Shi Shawara Kan Harkokin Siyasa
Daga Bello Wakili
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa Ibrahim Aminu Masari a matsayin Mai ba shi Shawara na Musamman kan Harkokin Siyasa.
Wata sanarwa da Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai Bayo Onanuga ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa an fara naɗa Masari a shekarar 2023 a matsayin Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Siyasa.
Kafin naɗin nasa, Ibrahim Kabiru Masari wanda ɗan asalin jihar Katsina ne, ya taɓa riƙe mukamin Sakataren jin dadi da walwala(Welfare Secretary) na jam’iyyar a lokacin jagorancin tsohon Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, .
Masari zai yi aiki ne tare da Alhaji Ya’u Darazau, wanda aka naɗa a matsayin Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Siyasa a watan Yulin 2023.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
