Labarai
Gwamnatin Jigawa Za Ta Kashe Miliyoyin Naira Don Sayen Gidaje 96 Daga Gwamnatin Tarayya
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Miliyan 853 domin sayen gidaje guda 96 daga gwamnatin tarayya.
Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Jihar da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Dutse.
A cewarsa, majalisar ta amince da sayen gidajen ne daga Ma’aikatar Gidaje da Raya Birane ta Tarayya.
Ya bayyana cewa sayen gidajen na da nufin magance matsalar matsuguni a cikin jihar, musamman ga ma’aikatan gwamnati da sauran waɗanda suka cancanta.
Ya ce shirin na daga cikin Ajandar Gwamna Umar Namadi 12, wadda ta ƙunshi babbar dabarar bunkasa gidaje da raya birane, domin samar da matsuguni mai kyau, rage gibin gidaje, da inganta rayuwar al’umma.
Wannan na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin na faɗaɗa damar samun gidaje masu araha da kuma kyautata jin daɗin jama’a.
Ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da kashe sama da Naira miliyan 914 domin ƙarin ayyuka a kan aikin gina hanyar Chuwasu zuwa Chakwaikwaiwa zuwa Zango Maje, wadda za ta haɗa da hanyar Yan Dutse zuwa Chori.
Sagir ya ce ƙarin ayyukan sun zama wajibi bayan ƙarin binciken fasaha da bitar aikin da aka gudanar, domin ƙara inganta ƙarfinsa da tsarin magudanan ruwa.
Ya ce majalisar ta ce sauyin da aka yi a cikin tsarin aikin zai tabbatar da cewa aikin ya cika ƙa’idojin da ake buƙata, tare da biyan buƙatun zirga-zirgar al’ummomin da za su amfana da shi.
Kwamishinan ya ƙara da cewa, da wannan amincewar, jimillar kuɗin kwangilar aikin ta kai sama da Naira Biliyan 5.4. Yana mai cewa hanyar Chuwasu zuwa Chakwaikwaiwa zuwa Zango Maje muhimmiyar hanya ce ta karkara wadda aka tsara domin inganta haɗin kai tsakanin al’umma, sauƙaƙa jigilar amfanin gona, ƙara samun damar isa kasuwanni, makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya, tare da bunƙasa tattalin arziƙi a yankin da abin ya shafa.
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai5 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai24 hours agoHukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai5 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai2 days agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
