Connect with us

Labarai

KAROTA Ta Sha Alwashin Ƙara Ƙarfafa Haɗin Kai da Jami’an Soji a Jihar Kano

Published

on

Daga Khadijah Aliyu 

Shugaban Hukumar Kula da Hanyoyi da Tsaron Ababen Hawa ta Jihar Kano,  (KAROTA), Faisal Mahmud Kabir, ya sake jaddada kudirinsa na inganta dangantaka mai kyau da haɗin kai da rundunonin soji da ke aiki a jihar Kano.

Faisal Mahmud ya sha alwashin hakan  ne yayin da ya karɓi baƙuncin Kwamandan 403 na makarantar horar da matukan jiragen sama da ke Kano, Group Captain Uchenna Ihediwa, a hedikwatar KAROTA.

Shugaban na KAROTA  ya amince cewa a wasu lokuta ana samun rashin fahimta tsakanin jami’an KAROTA da jami’an soji, amma ya tabbatar da cewa hukumar na aiki domin samar da hanyoyin warware duk wata takaddama cikin lumana.

Ya jaddada cewa burinsu shi ne tabbatar da kyakkyawar alaƙar aiki wadda za ta amfani jami’an tsaro da kuma al’umma baki ɗaya.

A nasa jawabin, Group Captain Uchenna Ihediwa ya ce ziyarar na da nufin ƙarfafa haɗin gwiwar da ke akwai tsakanin KAROTA da makarantar horas da matukan jiragen sojin sama, tare da mai da hankali kan tabbatar da doka da oda a hanyoyin jihar.

Ya jaddada muhimmancin haɗin kai, ƙwarewa, da kuma tsayawa tsayin daka ga dukkan jami’an tsaro domin tabbatar da kula da zirga-zirgar ababen hawa.

Kwamandan ya yabawa jami’an KAROTA bisa jajircewarsu da ƙwazon aikinsu, inda ya nuna buƙatar ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin hukumomi domin inganta tsaron jama’a da kuma tabbatar da bin dokokin zirga-zirga.

 

 

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara