Kasuwanci
Kungiyar Gwamnonin Nijeriya Ta Yi Alhini Ga Waɗanda Suka Rasu A Hare-Haren Ta’addanci
Kungiyar Gwamnonin Nijeriya ta bayyana damuwarta kan harin ta’addanci da aka kai daren Asabar a wasu al’umma uku na Tunga-Makeri, Konkoso da Pissa a Jihar Niger, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da sace wasu fararen hula marasa laifi.
A cikin wata sanarwa da Shugabanta kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya sanya wa hannu, kungiyar ta miƙa ta’aziyya ga al’ummar da gwamnatin Jihar Niger bisa wannan mummunan lamari.
Haka kuma, NGF ta jajanta wa al’ummar da gwamnatin Jihar Kwara kan sabon harin ta’addanci da aka kai a Woro da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama, inda aka kashe mutane da dama marasa laifi saboda sun ƙi amincewa da wata bakuwar akida da ba ta dace da koyarwar Musulunci ba.
Sanarwar ta kuma jajanta wa dukkan iyalan da suka rasa ’yan uwansu a waɗannan hare-haren ta’addanci marasa imani, tare da bayyana fahimta da goyon baya ga azabar da raɗaɗin da waɗanda suka tsira ke fuskanta. Haka nan ta yi addu’ar dawowar lafiya ga dukkan mutanen da har yanzu ba a san inda suke ba.
Kungiyar ta yaba wa jami’an tsaro bisa jarumtaka, nasarori da kuma gagarumar sadaukarwar da suke yi a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Sanarwar ta bukaci jami’an tsaro da su yi amfani da cikakken ikon gwamnati wajen murƙushe ’yan ta’adda da masu haɗa baki da su, tare da kawo ƙarshen wannan mummunan yanayi nan take.
A ƙarshe, NGF ta bayyana cikakken tabbaci ga ƙarfin jami’an tsaro na samun nasara a yaƙin da ake yi da ta’addanci, fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
