Ilimi
UNICEF Ta Bukaci a Gaggauta Inganta Ayyukan Ruwa da Tsaftar Muhalli a Makarantu da Asibitocin Kano da Jigawa
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Kula da Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ta yi kira da a dauki matakan gaggawa domin inganta ayyukan ruwa, tsafta da muhalli (WASH) a makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a jihohin Kano da Jigawa.
Babban Jami’in Ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Rihood Mohammed Farah, ne ya bayyana hakan yayin taron tattaunawa da kafafen yada labarai da masu ruwa da tsaki kan ayyukan WASH a jihohin biyu.
Farah ya ambato sakamakon binciken WASHNORM II na shekarar 2021, wanda ya nuna cewa kashi 11 cikin 100 ne kacal na makarantu a fadin kasar ke da damar samun muhimman ayyukan ruwa, tsafta da muhalli, yayin da kashi shida cikin 100 kawai na cibiyoyin lafiya ke cika wannan ka’ida.
Ya ce halin ya fi muni a yankunan karkara na Arewa maso Yammacin Najeriya, inda rashin wadatattun kayayyakin WASH ke sa miliyoyin yara kamuwa da cututtukan da za a iya karewa, kamar gudawa da kwalara.
A cewarsa, duk da cewa Jihar Jigawa ta samu ci gaba wajen kokarin zama jihar da ba a yin bahaya a fili, har yanzu kayayyakin wanke hannu da ingantattun gine-ginen tsafta a makarantu na karanci, lamarin da ke barazana ga lafiyar yara da karatunsu.
Mista Rahama Rihood Farah ya jaddada cewa makarantu da cibiyoyin lafiya da ba su da isassun ayyukan WASH na iya zama wuraren yaduwar cututtuka cikin sauri, lamarin da ke haddasa karuwar yawan daliban da ke fashin zuwa makaranta, musamman ‘yan mata.
Ya bayyana cewa munanan yanayin WASH na kawo cikas ga kokarin Najeriya na cimma Muradun Cigaban Mai Dorewa (SDGs) a fannin ilimi da samar da ruwan sha mai tsafta da tsaftar muhalli ga kowa.
Farah ya bayyana cewa tare da goyon bayan masu bayar da tallafi, UNICEF na aiki da gwamnatoci wajen inganta ayyukan WASH, ciki har da kaddamar da cibiyoyin lafiya da ilimi guda 84 masu jure sauyin yanayi a Kano da Jigawa, karkashin shirin CRIBS na fam miliyan 19 da Birtaniya ta dauki nauyi.
Ya kara da cewa an fadada shirin zuwa wasu jihohi bayan nasarar da ya samu a jihohin biyu.
Jami’in na UNICEF ya kuma jaddada muhimmancin kula da gyara da kula da kayayyakin WASH yadda ya kamata domin tabbatar da amfanin su na dogon lokaci.
Farah ya bukaci kafafen yada labarai da su taka rawar gani wajen fallasa gibin ayyukan WASH, sa ido kan kashe kudaden jama’a, rike hukumomi da kula da su, da kuma yin kira da a inganta kayayyaki a makarantu da cibiyoyin lafiya.
Ya ce ci gaba da fafutukar kafafen yada labarai na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da lafiyayyen muhallin koyo ga yara a fadin Arewa maso Yammacin Najeriya.
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
