Connect with us

Labarai

Ku Kyale Kananan Hukumomi Su Ci Gashin Kansu- Shugaba Tinubu

Published

on

Daga Bello Wakili 

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gargadi gwamnonin jihohi da su guji saba hukuncin Kotun Koli da ya bai wa ƙananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu game da kuɗadensu, yana mai gargaɗin cewa ci gaba da rashin bin hukuncin na iya jawo Gwamnatin Tarayya ta shiga tsakani.

Ya jaddada cewa dole ne a mutunta hukuncin tare da aiwatar da shi gaba ɗaya domin ƙarfafa shugabanci a matakin ƙananan hukumomi.

Shugaban ya bayar da wannan gargaɗi ne a yayin taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) karo na 15 na jam’iyyar APC, wanda aka gudanar a Cibiyar Taro ta Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Tinubu ya nuna damuwa kan yadda wasu gwamnatocin jihohi ke ci gaba da riƙe kuɗaɗen rabon da doka ta tanada da ya kamata a bai wa ƙananan hukumomi.

Ya bayyana cewa duk da ya zaɓi nuna haƙuri da girmamawa wajen mu’amala da gwamnonin, Gwamnatin Tarayya na da ikon tilasta bin doka.

Ya yi gargaɗin cewa idan gwamnonin suka ƙi bin hukuncin, Gwamnatin Tarayya na iya fara biyan kuɗaɗen ƙananan hukumomi kai tsaye daga Asusun Tarayya (Federation Account), bisa tanadin kundin tsarin mulki da kuma umarnin Kotun Koli.

Labarai

Labarai7 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai10 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai7 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara