Connect with us

Labarai

Burkina Faso: Shugaba Traoré Ya Gana Da Tawagar Najeriya

Published

on

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya aike da wata tawaga mai ƙarfi zuwa Burkina Faso domin tattauna batun matuƙan jirgin saman sojojin Najeriya da ake riƙe da su a ƙasar, sakamakon saukar gaggawa da jirginsu ya yi a ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.

Tawagar, ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ta gana da Shugaban Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, a Ouagadougou.

A yayin ganawar, Ambasada Tuggar ya miƙa saƙon gaisuwa da goyon baya daga Shugaba Tinubu ga Shugaba Traoré, tare da jaddada muhimmancin kyakkyawar alaƙa da makwabtaka tsakanin ƙasashen biyu.

Shugaban Burkina Faso ne ya tarbi tawagar tare da nuna godiya ga saƙon alheri daga Shugaban Najeriya.

Ɓangarorin biyu sun cimma matsaya cikin fahimta kan batun jami’an sojojin saman Najeriya da aka riƙe, inda aka amince da warware lamarin ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna.

Tawagar ta kuma kai ziyara wajen ganin halin da jami’an ke ciki, inda aka tabbatar da cewa suna cikin ƙoshin lafiya da ƙwarin gwiwa.

Tattaunawar ta kuma taɓo batutuwan ƙarfafa alaƙar siyasa da tsaro da tattalin arziƙi, tare da jaddada buƙatar haɗin gwiwa wajen tinkarar matsalolin tsaro da ke addabar yankin Sahel da Yammacin Afirka baki ɗaya.

A nasa ɓangaren, Ambasada Tuggar ya sake jaddada ƙudurin Najeriya na kyakkyawar makwabtaka da ci gaba da hulɗa da Burkina Faso, yana mai cewa ƙasar na goyon bayan duk wani yunƙuri da zai tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da bunƙasar tattalin arziki a yanki

Labarai

Labarai17 hours ago

Ana Zargin Mutum 140 Sun Bace Bayan Nutsewar Jirgin Ruwan Iran a Gaɓar Sri Lanka

Rundunar sojin ruwan Sri Lanka ta tabbatar da ceto mutum 32 bayan samun kiran gaggawa daga jirgin ruwan sojin Iran...

Ilimi17 hours ago

Gwamnatin Tarayya da ke Gusau za ta Kafa Cibiyar Nazari kan Tarihi da Al’adun Zamfara

Daga Aminu Dalhatu  Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Gusau (FUGUS), Farfesa Tukur Adamu, ya sanar da shirin jami’ar na kafa...

Labarai18 hours ago

Jam’iyyar APC Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni a Jihar Kano

Daga Abdullahi Jalaluddeen Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Kano ta zaɓi sabbin shugabanni domin jagorantar harkokin jam’iyyar. Zaɓen,...

Labarai20 hours ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Kashe Miliyoyin Naira Don Sayen Gidaje 96 Daga Gwamnatin Tarayya

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Miliyan 853 domin sayen gidaje guda...

Labarai2 days ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai3 days ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai3 days ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai3 days ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai3 days ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai3 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Mafi Shahara