Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Jinjinawa Gwamnan Jigawa Bisa Ayyukan Ci Gaban Jihar
Daga Usman Muhammad Zaria
Ministan Yada Labarai Alhaji Mohammed Idris, ya yabawa Gwamna Malam Umar Namadi bisa jagoranci na gaskiya da tsari, yana mai cewa Jihar Jigawa ta zama abin koyi wajen gudanar da mulki da kuma ingantaccen aiki a ma’aikatu.
Ministan ya yi wannan yabo ne lokacin wata ziyarar ban girma da ya kai wa gwamnan a Gidan Gwamnati da ke Dutse.

Muhammad Idris ya tuna da wata ziyarar da ya taba kaiwa Jigawa a baya, lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya domin duba harkokin noma. Ya ce yadda ya ga ana yin noman rani ya sa shi shauki game da irin ci gaban da ake samu a jihar.
Ya kuma bayyana godiyarsa kan kyakkyawan tarba da tawagarsa ta samu, yana mai cewa Jigawa jiha ce mai mutunci, zumunci da karimci.

Ministan ya kara tabbatar da aniyar gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wajen magance matsalolin tsaro da tattalin arziki, musamman ta hanyar gyaran da ake yi a rundunar tsaro domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.
A jawabinsa, Gwamna Namadi ya yi maraba da ministan da tawagarsa, yana mai bayyana cewa taron matasan APC na Arewa maso Yamma wata dama ce ta musayar ra’ayi game da mulki, ci gaba da kuma bunkasar matasa.

Ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen bunkasa karkokin matasa da mata a cikin tsarin shirye shiryenta na cigaban jihar.
“Muna goyon bayan mulikin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, Mutanen Jigawa suna tare da shi, muna goyon bayan shirin sa na ‘Renewed Hope’ domin gina Najeriya mai da hadin kai,” in ji gwamnan.
Daga nan sai gwamnan tare da ministoci suka halarci taron matasan APC na Arewa maso Yamma a Dutse, inda aka tattauna batutuwan shugabanci, gudunmawar da matasa ke badawa, da ci gaba mai dorewa.
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
