Labarai
Gidauniyar Abba Aliyu Ta Raba Kayan Solar Ga Al’umma A Kano
Gidauniyar Tallafawa Al’umma ta Abba Aliyu Gandu da ke jihar Kano ta bada horo sana’o’in hannu tare da raba tallafin Solar ga al’umma 500.
Wannan shi ne karo ba adadi da wannan gidauniyar ta shugaban hukumar Samarda Lantarki a yankunan Karkara Alhaji Abba Aliyu ta gudanar.
An raba kayan Solar guda 500 da kuma kudin fara sana’o’in hannu ga wadanda suka sami horo a karkashin wannan gidauniya.
Mataimakin Shugaban wannan gidauniya Suleiman Aliyu Abubakar ya bayyana cewa sama da shekara suna rana kyayyakin sun hada da solar domin kawo karshen matsalar wutar lantarki.
Suleiman Aliyu Abubakar wanda ya wakilci MD Abba Aliyu a wajen taron yace Kayayyakin sun hada da fanka da kayan caji da na haske a gidajen wadanda suka amfana da shirin.
A karshe ya hori wadanda suka amfana da wannan shirin kada su sayar da shi, kana su tabbatar sun yi amfani da shi yadda ya dace a wadannan kananan hukumomi uku da aka raba wannan tallafi a jihar Kano.
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
