Kasuwanci
Gwamnatin Tarayya Za Ta Farfado Da Filin Jirgin Sama Na Kano
Shugaban Hukumar Gudanarwa Filayen Jiragen Sama ta Kasa (FAAN), Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sake tabbatar da kudirin Gwamnatin Tarayya na dawo da tsohon martabar Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.
Dakta Ganduje ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar duba aiki da ya kai filin jirgin a Kano.
Ya jagoranci wata tawaga mai ƙarfi ta jami’an FAAN domin tantance halin da filin jirgin yake ciki yanzu, ciki har da ayyukan da ake gudanarwa da kuma waɗanda aka bari da nufin samar da cikakken tsari na zamani da dorewar ci gaba.
Ya bayyana a matsayin ɗaya daga cikin tsofaffin filayen jiragen sama masu tarihi a Najeriya da yankin Yammacin Afirka, wanda a da yake ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin tashi da saukar jirage da ke haɗa Najeriya da sauran sassan duniya.
“Mun zo ne mu gani da idonmu, tsoffin ayyuka da sababbi, domin mu tsara sabuwar hanya ta farfado da wannan fili tare da dawo da matsayinsa cikin fitattun filayen jiragen sama na yankin,” in ji Ganduje.
Ya jaddada cewa hukumar FAAN za ta tabbatar da inganta jin daɗin fasinjoji, kiyaye ƙa’idodin tsaro, da kuma haɓaka ingancin aiki bisa ka’idodin ƙasa da ƙasa.
Dakta Ganduje ya tabbatar da cewa abubuwan da tawagar ta gano a yayin ziyarar za su zama ginshiƙi wajen tsara sabuwar manuniya ta dabarun sake farfado da filin domin ya zama abin koyi a harkar gudanar da filayen jiragen sama da kuma abin ƙarfafa tattalin arzikin Arewa.
Tawagar ta ziyarci sassa daban-daban na filin jirgin, ciki har da zauren sauka da tashin fasinjoji, hanyar tashi da saukar jirage, da kuma rukunin jigilar kaya, domin gano wuraren da ake bukatar gaggawar gyara.
ABDULLAHI JALALUDDEEN, Kano.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
