Connect with us

Labarai

Marasa Lafiya A Nasarawa Sun Koka Game Da Yajin Aikin Likitoci

Published

on

Daga Aliyu Muraki

Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa  ta Kasa reshen Jihar Nasarawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya Lafia ta bi umarnin ƙungiyar ta ƙasa wajen shiga yajin aiki na ɗindindin.

Wakilinmu wanda ya ziyarci asibitin koyarwar, ya bayar da rahoton cewa likitocin sun bar wuraren aikinsu domin matsin lamba ga gwamnatin tarayya ta biya dukkan hakkokinsu da ke karuwa zuwa biliyoyin naira.

A yayin ziyarar, ya ruwaito cewa nas nas da ungozoma ne kawai ke kula da marasa lafiya, musamman a sashen bada kulawar gaggawa,  inda suke ƙoƙarin taimaka wa waɗanda ke cikin mawuyacin hali, yayin da ake tura waɗanda lamuransu ke neman kulawar likitoci zuwa wasu asibitoci domin samun kulawar gaggawa.

Haka zalika su ma likitocin  Asibitin Kula da Lafiya na Tarayya (FMC) KKeffisun bi sahun takwarorinsu wajen shiga yajin aikin.

Hakan ya tilastawa  marasa lafiya barin asibitocin domin komawa asibitoci masu zaman kansu a cikin biranen biyu, yayin da wasu kuma suka koma gida suna jiran tsammani.

A tattaunawa da wasu marasa lafiya, Gloria Namo da Jamil Ishaq, da ke jinya a asibitocin, sun bayyana damuwarsu kan yadda gwamnatin tarayya ta kasa biyan bukatun likitocin, wanda hakan ya hana su ci gaba da samun kulawa.

Sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta biyan dukkan haƙƙin likitocin, ganin cewa ba za su iya zuwa asibitoci masu zaman kansu ba saboda tsadar rayuwa.

Labarai

Labarai16 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai18 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai7 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara