Labarai
Shugaba Tinubu ya Ayyana Masu Garkuwa da Mutane a Matsayin Yan ta’adda
Shugaban Kasar Nijeriya Ahmed Bola Tinubu ya bayyana cewa ya zama dole a riƙa ɗaukan mutanen da ke da hannu a aikata miyagun laifuka a matsayin ƴan ta’adda.
Shugaban ya bayyana haka ne ranar Talata a taron buɗe-baki tare da ma’aikatan shari’a na gwamnatin tarayya bisa jagorancin alƙalin alƙalai na ƙasa, mai shari’a Olukayode Ariwoola.

Da yake nanata ƙudirin gwamnati na murƙushe ƴan bindiga, shugaba Tinubu ya ce waɗanda suke sace yara matsorata ne da ba za su iya gaba da gaba da sojojin Najeriya ba.
“Dole ne mu ayyana masu garkuwa a matsayin ƴan ta’adda,” in ji shugaban ƙasar, kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa Ajuri Ngelale ta ruwaito.
Bello WAKILI
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai22 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
