Labarai
Gwamnatin Jigawa Na Aikin Tituna Na Miliyoyin Kudi A Karamar Hukumar Malam Madori
Gwamnatin Jihar Jigawa ta kashe sama da Naira Biliyan 18 da rabi wajen gina titin Arbus zuwa Girbobo zuwa Garin Bukar, da ke karamar hukumar Malam Madori, mai tsawon kilomita 33 da rabi.
Mai Bai wa Gwamna Shawara na Musamman kan Kula da Ayyuka, Alhaji Usman Haladu Kanya ne ya bayyana hakan ga manema labarai yayin ziyarar duba wasu ayyukan hanyoyi da ake gudanarwa a kananan hukumomin Kiyawa, Kafin Hausa, Hadejia da Malam Madori.
Haladu Kanya wanda ya jagoranci tawagar masu ruwa da tsaki da kuma injiniyoyin hukumar kula da aiwatar da ayyuka ta jihar zuwa wuraren ayyukan, ya kuma duba titin Andaza zuwa Duhuwa zuwa Katanga.
Sauran ayyukan da aka ziyarta sun haɗa da titin cikin garin Bulangu, da na hanyar jami’ar Assalam, da gyaran hanyar Balago zuwa Auno da sauransu.
Alhaji Usman Haladu Kanya ya gode wa Gwamna Umar Namadi bisa kaddamarwa da kuma aiwatar da muhimman ayyukan ci gaban al’umma.
Ya kuma yi kira ga jama’ar jihar da su ci gaba da mara wa manufofi da shirye-shiryen gwamnati baya.
Usman Muhammad Zaria
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
