Labarai
Arewa Cohesion Ta Kaddamar da Shuwagabani Na Jihohi Da Kwamitoci Don Inganta Hadin Kai Da Cigaba
Kungiyar Arewa Cohesion for Peace, Unity and Development Initiative ta kaddamar da shuwagabanin jihohi da kwamitoci na dindindin domin ƙarfafa tushen aikin kungiyar.
Daraktan Gidauniyar, Dr. Abdullahi Idris, ne ya bayyana haka a wajen bikin kaddamarwar da aka gudanar a Arewa House, Kaduna.
Kwamitocin da aka kaddamar sun haɗa da: kwamitin tsare-tsare da dabaru, kwamitin kudi da kwamitin kula da Jama’a, tare da shuwagabanin jihohi na rikon kwarya na kungiyar.
Dr. Abdullahi Idris ya bayyana cewa waɗannan sabon tsarin zai taimaka wajen ganin kungiyar ta zauna yanda ya kamata da hangen nesa da zaman lafiya, haɗin kai, da ci gaba mai ɗaurewa a Arewacin Najeriya.
Ya kuma yi bayanin ayyukansu kamar haka, Kwamitin Tsare-tsare da Dabaru zai kula da tsara manufofi, fifita manyan ayyuka, da gano abokan hulɗa don tabbatar da cimma manufofin kungiyar.
A kan Kwamitin Kudi kuwa, ya jaddada muhimmancin tara kudade, yin amfani da su cikin hikima, tare da kiyaye gaskiya da lissafi na nagarta.
Dr. Abdullahi Idris ya tabbatar da cewa dorewar kudi da kyakkyawan gudanarwa ne za su tabbatar da nasarar kungiyar nan gaba.
Haka kuma ya jaddada muhimmancin Kwamitin Hula da Jama’a, inda ya bayyana shi a matsayin murya da hoto na kungiyar.
A cewarsa, kwamitin zai inganta sunan kungiyar a idon jama’a, ya yaƙi labaran ƙarya, ya kuma tabbatar da ingantacciyar kafuwa a kafofin yada labarai na gargajiya da na zamani, domin Arewa Cohesion ta zama suna sananne a cikin gida da wajen gida.
Game da matakin ƙasa kuwa, Daraktan ya haskaka rawar da Kwamishinonin Jihohi za su taka, inda ya ce su ne za su sauke hangen nesa na kungiyar zuwa kowace jiha, ƙaramar hukuma da kuma gunduma.
Ya bayyana cewa aikinsu ya haɗa da tara mambobi, kafa tsare-tsare masu haɗa kowa da kowa, da tabbatar da cewa mata, matasa, tsofaffi da kuma masu nakasa sun samu wakilci a kowane reshe na jihohi.
Ya ƙara da cewa nadin kwamishinonin jihohi zai ɗauki watanni 12 a matsayin gwaji, daga bisani kuma nagarta da sadaukarwa za su tantance sahihancin mukamansu.
Yayin kaddamar da kwamitoci da kwamishinonin, Dr. Idris ya tunatar da su cewa an zaɓe su ne bisa ƙwarewa, gaskiya da sadaukarwa, ba saboda sa’a ba.
Ya shawarce su da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya, tawali’u da ladabi, yana mai jaddada cewa nasarar kungiyar ta dogara da yadda za su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.
COV: Adamu Yusuf
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
